Yana kasancewa da wani aiki da Bush bai gama ba tukuna a ziyararsa ta wannan karo. Har zuwa karshen ziyarar Bush a Afirka, ya zuwa yanzu dai ba a tabbatar da wurin da za a kafa hedkwatar sojojin Amurka a Afirka ba tukuna. Ko da yake Amurka ta sha aikawa da manyan jami'anta zuwa kasashen Afirka domin shawo kansu da su amince da shirin Amurka na kafa hedkwatar sojojin Amurka a Afirka, amma a halin yanzu sai Liberia kawai a bayyane ne ta bayyana fatanta na amincewa da hedkwatar sojojin Amurka a Afirka.
A lokacin ziyararsa, Bush ya sha yin karin bayani da cewa, kasarsa ba ta yi shirin kafa sabon sansanin soja a Afirka ba, nufin Amurka na kafa hedkwatarta ta sojoji a Afirka shi ne domin taimakawa kasashen Afirka wajen inganta karfinsu na kiyaye zaman lafiya da yaki da fasa-kwauri da kuma yaki da ta'addanci kawai. Amma ga alama Ghana da sauran kasashen Afirka suna nuna shakku sosai. A Liberia, kasa ce ta karshe da Bush ya kai ziyara, dukan bangarorin 2 ba su yi jawabi a bayyane kan batun zaben wurin kafa hedkwatar sojojin Amurka a Afirka ba. Bayan tashin Bush, shugaban Tanzania ya yi jawabin cewa, Tanzania ba ta da karfin kafa hedkwatar sojojin Amurka a Afirka ba. Don haka, cikin sauki ne muka iya gano cewa, ya zuwa yanzu dai kasashen Afirka ba su kwanta da hankulansu kan Amurka ba tukuna.
Bayan nazarin ziyarar Bush a wannan karo, wasu manazarta sun nuna cewa, nan gaba Amurka za ta kara ba da tasirinta a Afirka a harkokin siyasa da tattalin arziki, za ta ci gaba da karfafa habaka makamashi a Afirka, za ta kuma dauki matakai daban daban domin tabbatar da samun isasshen makamashi daga Afirka. A takaice dai, Afirka ta riga ta zama muhimmin bangare na manyan tsare-tsare da Amurka ke aiwatarwa a duk duniya.(Tasallah) 1 2
|