Ran 21 ga wata, shugaba Bush na kasar Amurka ya gama ziyararsa ta mako guda a kasashe 5 na Afirka, wato Benin da Tanzania da Ruwanda da Ghana da kuma Liberia. Mr. Bush ya yi wannan ziyara ne bisa dalilai da dama, a ciki har da shawo kan wadannan kasashe game da amincewa da kafa hedkwatar sojojin Amurka a Afirka, da kara yin bayani kan manufofin Amurka kan Afirka, da neman zumunci da kuma goyon bayan daga kasashen Afirka ta hanyar kara samar musu taimako da dai sauransu, amma ya zuwa yanzu dai sakamakon da ya samu ya yi kadan.
A cikin jawabinsa da ya bayar kafin tashinsa, Mr. Bush ya bayyana cewa, Afirka tana da muhimmanci sosai wajen tabbatar da moriyar Amurka bisa manyan tsare-tsare. Halin da ake ciki a Afirka ya kan ba da tasiri kan tsaron Amurka kai tsaye. A lokacin ziyararsa a Afirka, Bush ya kuma jaddada cewa, yanzu ba Afirka be ce take bukatar Afirka, a'a, Amurka ta fi bukatar Afirka. Yanzu yawan man fetur da Amurka ta shigo daga Afirka ya wuce kashi 15 cikin kashi dari, bisa yawan da ta shigo daga ketare. Tsarin leken asiri na Amurka ya kiyasta cewa, a shekarar 2015, irin wadannan adadi zai kai misalin kashi 25 cikin kashi dari. Haka kuma, yawan jarin da Amurka za ta zuba kan harkokin man fetur zai wuce kashi 2 cikin kashi 3 bisa yawan jarin da ta zuba kan Afirka.
Bayan yakin cacar baki, gwamnatocin Amurka na zagaye da yawa sun tsara manufofi kan Afirka a bayyane. Gwamnatin George Herbert Walker Bush ta fi dora muhimmanci kan mamaye wuraren da kasar Soviet Union ta bari da kuma yada dimokuradiyya a Afirka. Gwamnatin Clinton ta jaddada raya hulda a tsakaninta da Afirka ta hanyar bunkasa tattalin arziki da ciniki. Bayan da George W. Bush ya fara mulkin Amurka, ya canza manuforta zuwa yaki da ta'addanci da kuma kwace makamashi.
Saboda Amurka ta nemi samun karin moriya daga Afirka, shi ya sa Bush ya yi ta kara bai wa Afirka taimako bayan da ya fara mulkin fadar gwamnatin wato White House a shekarar 2001.
Mun iya gano muhimmancin da Amurka take nunawa kan Afirka a cikin manufarta bisa wadannan kasashe 5 na Afirka da ya zaba a tsanake don kai ziyara. Benin da Tanzania da Ruwanda da Ghana da Liberia wasunsu suna matsayin muhimman wurare bisa manyan tsare-tsare saboda suna bakin tekun Atlantic, wasunsu kuma suna dab da yankunan Afirka da ke jawo hankulan kasashen duniya, shi ya sa Amurka ta nuna kulawa a kansu domin tabbatar da moriyarta.
1 2
|