Sin ciki da waje (chinaabc)Rediyon kasar SinSashen Hausa
China Radio International
Labarun gida
Labarun duniya
Labarun Siyasa
Labarun Tattalin Arziki
Labarun Al'adu
Labarun Wasanni
Sauran Labaru
Saurari labarai da dumi-duminsu da sauran shirye-shirye
more>>
[ Al'adu ]
 --Al'adun Sinawa
 --Kabilun kasar Sin
[ Bunkasuwa ]
 --Tattalin arziki
 --Bunkasuwar Sin
[ Yawon shakatawa ]
 --Yawo a kasar Sin
 --Wurare masu yawo
[ Ilmi, Lafiya ]
 --Fagen bincike
 --Kiwon lafiya
[ Wasanni ]
 --Labaran wasannin
 --Me ka sani
(GMT+08:00) 2008-02-22 15:46:38    
Maganin gargajiya na kasar Sin

cri

Magungunan gargajiyar kasar Sin sun yi yawa, kuma a kan bi hanyar musamman wajen yin maganin. Ko wane irin maganin kuma, ya kan hada da tsire-tsire fiye da goma. Wasu ana yin su cikin kwayoyi, wasu kuwa ana tafasa su a cikin ruwa, sa'an nan a sha ruwan. Magungunan gargajiyar kasar Sin suna da amfani mai kyau, kuma yawanci ba su da illa sosai. Bisa nazarin da aka yi kuma, an ce, magungunan gargajiya na kasar Sin suna da amfanin musamman ga wasu cututtuka masu tsanani wadanda ake fama da su har ma a zamanin yanzu.

A nan kasar Sin, akwai shahararrun masana'antun maganin gargajiya masu yawa, kuma ana sayar da magungunan da suke masana'anta har zuwa kasashen kudu maso gabashin Asiya da kuma kasashen Turai da Amurka da dai sauransu. Tuni a karni na biyu kafin haihuwar Annabi Isa alaihissalam, Turai ta riga ta shigar da wani maganin gargajiya da ake kira Dahuang wanda ake iya samunsa musamman ma a kasar Sin. A shekaru fiye da 1300 da suka wuce kuma, masanan ilmin maganin gargajiyar kasar Sin sun sa sawunsu har zuwa kudu maso gabashin Asiya don ilmantar da jama'a a kan ilmin magani, sun kuma tafi tare da maganin gargajiya na kasar Sin.

Maganin gargajiya arziki ne al'adun kasar Sin, haka kuma wani muhimmin kashi ne na magungunan duniya. Sabo da kyakkyawan amfaninsa, ya sami karbuwa sosai a kasashen duniya. Gwamnatin kasar Sin na dora muhimmanci sosai a kan bunkasa maganin gargajiya, kuma tana hada gwiwa da gamayyar kasa da kasa, ta yadda maganin zai kara taka gaggarumar rawa a wajen taimaka wa dan Adam yaki da cututtuka iri iri.

To, masu sauraro, wannan shi ya kawo karshen bayanin da muka yi dangane da maganin gargajiyar kasar Sin. Tare da fatan kun ji dadin bayanin, kuma za ku ci gaba da rubuto mana wasiku da kuma sauraron shirinmu na amsoshin wasikunku, ni Lubabatu da na gabatar daga nan Beijing ke cewa, sai mako mai zuwa, idan Allah ya kai mu.(Lubabatu Lei)


1 2