Sin ciki da waje (chinaabc)Rediyon kasar SinSashen Hausa
China Radio International
Labarun gida
Labarun duniya
Labarun Siyasa
Labarun Tattalin Arziki
Labarun Al'adu
Labarun Wasanni
Sauran Labaru
Saurari labarai da dumi-duminsu da sauran shirye-shirye
more>>
[ Al'adu ]
 --Al'adun Sinawa
 --Kabilun kasar Sin
[ Bunkasuwa ]
 --Tattalin arziki
 --Bunkasuwar Sin
[ Yawon shakatawa ]
 --Yawo a kasar Sin
 --Wurare masu yawo
[ Ilmi, Lafiya ]
 --Fagen bincike
 --Kiwon lafiya
[ Wasanni ]
 --Labaran wasannin
 --Me ka sani
(GMT+08:00) 2008-02-22 15:46:38    
Maganin gargajiya na kasar Sin

cri

Tambayar da za mu amsa a wannan mako ta fito ne daga hannun malam Aliyu Usman, wanda ya turo mana wasikar da ke cewa, ina so in samu karin bayani game da maganin gargajiya na kasar Sin. Watakila akwai masu sauraronmu da suka taba sha maganin gargajiya na kasar Sin, har ma sun ce, "kai, maganin gargajiya na kasar Sin na da amfani mai ban mamaki!" To, sabo da haka, masu karatu, yanzu bari mu dan bayyana muku tarihin maganin gargajiya na kasar Sin.

Kasar Sin tana daya daga cikin kasashen da suka fi dadadden tarihi a duniya, kuma ta yi arziki a fannin kimiyya da al'adu, kuma maganin gargajiya na kasar na daya daga cikinsu.

Bisa takardun tarihi, an ce, tuni a shekaru fiye da 3000 da suka wuce, Sinawa sun fara yin amfani da maganin gargajiya wajen yaki da cututtuka iri daban daban. A shekaru aru aru da suka wuce, mutanen Sin sun rayu bisa kamun kifi da farauta, kuma suna dibar 'ya'yan itatuwa da tsire-tsire domin su ci. Bayan da suka ci wadannan abubuwa, sai su kan gane cewa, abubuwa iri daban daban suna da amfani daban daban ga jikin dan Adam. A cikin lokaci mai tsawo, sannu a hankali ne suka fara samun ilmi da kuma fasaha dangane da yadda za a bambanta amfanin wadannan tsire-tsire, kuma suka fara yin amfani da su a fannin jiyya da kiwon lafiya. A kai a kai ne kuma, wadannan tsire-tsire suka zama magunguna. Wannan shi ne asalin maganin gargajiya na kasar Sin.

Sabo da kasar Sin tana da fadi sosai, shi ya sa tana da arzikin magungunan sha na gargajiya masu yawa. Ya zuwa yanzu dai, yawan magungunan gargajiyar kasar Sin da aka gano ya riga ya kai sama da dubu 5.


1 2