Sin ciki da waje (chinaabc)Rediyon kasar SinSashen Hausa
China Radio International
Labarun gida
Labarun duniya
Labarun Siyasa
Labarun Tattalin Arziki
Labarun Al'adu
Labarun Wasanni
Sauran Labaru
Saurari labarai da dumi-duminsu da sauran shirye-shirye
more>>
[ Al'adu ]
 --Al'adun Sinawa
 --Kabilun kasar Sin
[ Bunkasuwa ]
 --Tattalin arziki
 --Bunkasuwar Sin
[ Yawon shakatawa ]
 --Yawo a kasar Sin
 --Wurare masu yawo
[ Ilmi, Lafiya ]
 --Fagen bincike
 --Kiwon lafiya
[ Wasanni ]
 --Labaran wasannin
 --Me ka sani
(GMT+08:00) 2008-02-20 12:40:57    
Tuka mota cikin dogon lokaci da rana zai kara hadarin kamuwa da sankarar fata

cri

Scott Fosco, kwararre a fannin ilmin fata mai kula da binciken ya bayyana cewa, sun gudanar da wani binciken daban ga kasashen da kujerun tuka motoci suke a gafen dama, daga baya kuma suka gano cewa, game da wadanda su kan tuka motoci cikin dogon lokaci da rana na wadannan kasashe, hadarin kamuwa da ciwon sankarar fata ya samu karuwa, haka kuma su kan kamu da ciwon a bangaren dama na jikinsu.

Manazarta na kasar Amurka sun bayyana cewa, bayan da suka yi nazari, sun gano cewa, idan yawan karuwar kiba da aka samu, sai yawan karuwar yiyuwar daina sanya damarar ceto da aka yi lokacin da yake tuka mota. Alal misali, kashi 55 bisa dari daga cikin mutanen da suke samun kiba fiye da kima kwarai da gaske ba su son sanya damarar ceto. Kuma dukkansu suna ganin cewa, dalilin da ya sa haka shi ne sabo da mai yiyuwa ne mutanen da suke samun kiba fiye da kima ba su ji dadi sosai in suka sanya damarar ceto.

Wani manazarci na jami'ar Vanderbilt ta kasar Amurka da ya kula da nazarin ya bayyana cewa, sanin kowa, samun kiba fiye da kima zai haddasa cututtukan zuciya da hauhawar jini da cutar sukari da wasu ire-iren sankara, amma yanzu ya kamata a kara da cewa, samun kiba fiye da kima zai kara hadarin tuka mota, mutanen da suke samun kiba fiye da kima sun fi saukin jikkata ko mutuwa a cikin hadarin mota.

Sabo da haka manazarta suna fatan za a iya mai da hankali a kan wannan nazari, ta haka za a iya sa kaimi ga mutanen da suke samun kiba fiye da kima wajen sanya damarar ceto bisa son rai.(Kande Gao)


1 2