Sin ciki da waje (chinaabc)Rediyon kasar SinSashen Hausa
China Radio International
Labarun gida
Labarun duniya
Labarun Siyasa
Labarun Tattalin Arziki
Labarun Al'adu
Labarun Wasanni
Sauran Labaru
Saurari labarai da dumi-duminsu da sauran shirye-shirye
more>>
[ Al'adu ]
 --Al'adun Sinawa
 --Kabilun kasar Sin
[ Bunkasuwa ]
 --Tattalin arziki
 --Bunkasuwar Sin
[ Yawon shakatawa ]
 --Yawo a kasar Sin
 --Wurare masu yawo
[ Ilmi, Lafiya ]
 --Fagen bincike
 --Kiwon lafiya
[ Wasanni ]
 --Labaran wasannin
 --Me ka sani
(GMT+08:00) 2008-02-20 12:40:57    
Tuka mota cikin dogon lokaci da rana zai kara hadarin kamuwa da sankarar fata

cri

Manazarta na kwalejin ilmin likitanci na jami'ar Saint Louis ta kasar Amurka sun gano cewa, game da mutane da su kan tuka mota cikin dogon lokaci a cikin zafin rana, hadarin kamuwa da ciwon sankarar fata zai karu gare su. Dalilin da ya sa haka shi ne sabo da fuska da hannunsu su kan sha hasken rana.

Bisa labarin da kafofin watsa labarai na kasar Amurka suka bayar a ran 6 ga wata, an ce, a cikin rahoton da suka gabatar ga taron shekara shekara kan ilmin kimiyya na fata na kasar Amurka a kwanan nan, manazarta sun bayyana cewa, yanzu yawancin gilas na motoci suna iya bayar da kariya sinadarin hasken ultraviolet maras karfi, amma ba su iya kare sinadarin hasken ultraviolet mai matukar karfi da kuma sauran sinadarin hasken rana. Sabo da haka, game da mutanen da su kan tuka motoci na dogon lokaci a karkashin hasken rana, musamman ma wadanda su kan bude tagogi lokacin da suke tuka motoci, sun fi saukin samun sinadarin hasken ultraviolet.

Bayan da manazarta suka gudanar da bincike kan mutane masu fama da ciwon sankarar fata na Amurka da yawansu ya kai 898, sun gano cewa, kashi 53 cikin dari daga cikinsu sun kamu da ciwon sankarar fata a bangaren hagu na jikinsu, dalilin da ya sa haka shi ne sabo da bangaren hagun jikinsu ya kan fuskanci hasken rana lokacin da ake tuka mota. Ban da wannan kuma kashi 64 cikin dari daga cikin wadannan mutane maza ne, dalilin da ya sa haka shi ne sabo da maza sun fi tuka motoci cikin dogon lokaci da rana idan an kwatanta da mata.


1 2