Ran 13 ga wata, agogon wurin, a birnin Zurich na kasar Switzerland, wato hedkwatar kungiyar wasan kwallon kafa ta duniya, kungiyar wasan kwallon kafa ta duniya ta sanar da sabon jerin sunayen kungiyoyin kasashen duniya na wasan kwallon kafa na maza, a cikin jerin sunayen, kungiyar kasar Sin ta sami ci gaba wato ta zama lamba ta 75, ban da wannan kuma, kamar yadda kuka sani, kungiyar kasar Argentina da ta kasar Brazil da kuma ta kasar Italiya sun zama uku na gaba.
Ran 18 ga wata, a New Orleans na kasar Amurka, aka rufe gasar 'yan wasan tauraro ta wannan shekarar gasa ta gasar kwallon kwando ta sana'a ta kasar Amurka wato NBA, a gun gasar, kungiyar 'yan wasan tauraro ta gabashin kasar ta lashe kungiyar yammacin kasar. 'Dan wasa na kungiyar 'yan wasan taoraro ta gabashin kasar Lebron James ya ci zaben 'dan wasa mafi daraja na gasar.
Ran 17 ga wata, agogon wurin, a kasar Holand, aka rufe gasar cin kofin Turai tsakanin kungiya kungiya ta wasan kwallon badminton ta shekarar 2008, a gun zagaye na karshe na gasar, kungiyar maza ta kasar Denmark ta lashe kungiyar maza ta kasar Ingila ta zama zakara. Ban da wannan kuma, kungiyar mata ta kasar Denmark ta lashe kungiyar mata ta kasar Holand, ita ma ta zama zakara.(Jamila Zhou) 1 2
|