Sin ciki da waje (chinaabc)Rediyon kasar SinSashen Hausa
China Radio International
Labarun gida
Labarun duniya
Labarun Siyasa
Labarun Tattalin Arziki
Labarun Al'adu
Labarun Wasanni
Sauran Labaru
Saurari labarai da dumi-duminsu da sauran shirye-shirye
more>>
[ Al'adu ]
 --Al'adun Sinawa
 --Kabilun kasar Sin
[ Bunkasuwa ]
 --Tattalin arziki
 --Bunkasuwar Sin
[ Yawon shakatawa ]
 --Yawo a kasar Sin
 --Wurare masu yawo
[ Ilmi, Lafiya ]
 --Fagen bincike
 --Kiwon lafiya
[ Wasanni ]
 --Labaran wasannin
 --Me ka sani
(GMT+08:00) 2008-02-20 09:04:24    
Wasu labaru game da wasannin motsa jiki (13/02-19/02)

cri

Ya zuwa ran 12 ga wata, gaba daya mutane wadanda suka yi rajista domin aikin sa kai na gasar wasannin Olympic ta birnin Beijing da gasar wasannin Olympic ta nakasassu ta birnin Beijing sun riga sun zarce dubu dari tara da talatin, wato sun fi yawa a tarihin gasar wasannin Olympic. Sashen kula da masu aikin sa kai na kwamitin shirya gasar wasannin Olympic ta birnin Beijing ya fara aikin hayar masu aikin sa kai ne daga watan Agusta na shekarar 2006, kuma zai yi hayar masu aikin sa kai a duk fadin duniya.

Ran 17 ga wata, aka fara gasar cin kofin gabashin Asiya ta wasan kwallon kafa ta shekarar 2008 a birnin Chongqing dake kudu maso yammacin kasar Sin, a gun gasa ta farko, kungiyar maza ta kasar Korea ta kudu ta lashe kungiyar kasar Sin. Gaba daya kungiyoyi takwas wato kungiyoyin maza hudu da na mata hudu da suka zo daga kasashe hudu wato kasar korea ta arewa da ta korea ta kudu da kasar Japan da kuma kasar Sin sun halarci wannan gasa. Kuma za a kammala gasar a ran 24 ga wata.


1 2