A ganin Mr Yuan Gangming kuma, a yayin da gwamnatin kasar Sin take tafiyar da manufofin sarrafa tattalin arziki, kamata ya yi gwamnati ta nuna goyon baya ga sha'anonin noman hatsi, da kiwon dabbobi, domin kara samar da kayayyaki, ta yadda za a iya sassauta matsin daga karuwar farashin kayayyaki. Game da haka, Mr Yuan ya ce,
'A halni yanzu, kamata ya yi manufofinmu su tabbatar da kara samun kayayyaki masu yawa, ba wai karuwar farashin kayayyaki za ta haddasar bunkasuwar tattalin arziki cikin sauri fiye da kimma ba.'
Ban da wannan kuma, Mr Yuan Gangming yana kyautata zaton cewa, gwamnatin kasar Sin za ta ci gaba da tafiyar da manufofin sarrafa bunkasuwar tattalin arziki, a sakamakon haka, yawan karuwar farashin kayayyaki zai ragu a wata mai zuwa. Yawan karuwar farashin kayayyaki a duk shekarar 2008 kuma zai kai kashi 6 zuwa 7 daga cikin dari, yawan karuwar tattalin arzikin kasar Sin zai kai kashi 11 daga cikin dari.(Danladi) 1 2
|