Sin ciki da waje (chinaabc)Rediyon kasar SinSashen Hausa
China Radio International
Labarun gida
Labarun duniya
Labarun Siyasa
Labarun Tattalin Arziki
Labarun Al'adu
Labarun Wasanni
Sauran Labaru
Saurari labarai da dumi-duminsu da sauran shirye-shirye
more>>
[ Al'adu ]
 --Al'adun Sinawa
 --Kabilun kasar Sin
[ Bunkasuwa ]
 --Tattalin arziki
 --Bunkasuwar Sin
[ Yawon shakatawa ]
 --Yawo a kasar Sin
 --Wurare masu yawo
[ Ilmi, Lafiya ]
 --Fagen bincike
 --Kiwon lafiya
[ Wasanni ]
 --Labaran wasannin
 --Me ka sani
(GMT+08:00) 2008-02-19 17:37:08    
A watan jiya, farashin kayayyaki na zaman yau da kullum na mazaunan kasar Sin ya kai sabon matsayin koli

cri

A ran 19 ga wata, hukumar kididdiga ta kasar Sin ta bayar da farashin kayayyaki na zaman yau da kullum na mazaunan kasar Sin na watan watan Janairu na shekarar bana, yawan karuwarsa ya kai kashi 7.1 daga cikin dari, wanda ya kai sabon matsayin koli tun bayan shekarar 1997. Game da haka, shehun malami daga hukumar nazarin sha'anin kudi da kuma takardun shaidar kudi ta Jami'ar jama'a ta kasar Sin wato Mr Zhao Xijun ya gaya mana cewa,

'Karuwar farashin kayayyaki ta zo ne daga karuwar farashi na wasu danyun kayayyaki da abinci a shekarar da ta wuce. Ban da wannan kuma, a cikin shekarar bara, farashin hatsi da ma'adinai da mai sun karu sosai, kasar Sin ta shigo da su da yawa daga kasashen waje, sabo da haka ne, farashin kayayyaki na wata Janairu na bana ya karu sosai.'

Game da haka kuma, masanin tattalin arziki na cibiyar nazarin harkokin rayuwar jama'a ta kasar Sin wato Mr Yuan Gangming ya bayyana cewa,

'Wani muhimmin dalili daban shi ne, domin bala'un ruwan sama da dusar kankara sun haddasa karuwar farashin kayayyaki. Idan babu irin wadannan bala'u, mai yiyuwa ne farashin kayayyaki zai ragu, idan aka kwatanta shi da na watan Disamba na shekarar bara.'

Game da karuwar farashin kayayyaki cikin sauri, bangarori daban daban suna mai da hankali sosai kan manufofin tattalin arzikin daga gwamnatin kasar Sin. Wasu suna ganin cewa, kamata ya yi bankin tsakiya na kasar Sin ya kara yawan kudin ruwa da yawan kason kudin ajiya da hukumomin kudi suka ajiye a wurinsa. Mr Zhao Xijun ya yarda da haka, ya ce,

'A ganina, a halin yanzu dai, muna fuskantar matsi daga hauhawar farashin kaya, kamata ya yi manufofin kudi na gwamnati su kawar da irin wannan matsi.'


1 2