Sin ciki da waje (chinaabc)Rediyon kasar SinSashen Hausa
China Radio International
Labarun gida
Labarun duniya
Labarun Siyasa
Labarun Tattalin Arziki
Labarun Al'adu
Labarun Wasanni
Sauran Labaru
Saurari labarai da dumi-duminsu da sauran shirye-shirye
more>>
[ Al'adu ]
 --Al'adun Sinawa
 --Kabilun kasar Sin
[ Bunkasuwa ]
 --Tattalin arziki
 --Bunkasuwar Sin
[ Yawon shakatawa ]
 --Yawo a kasar Sin
 --Wurare masu yawo
[ Ilmi, Lafiya ]
 --Fagen bincike
 --Kiwon lafiya
[ Wasanni ]
 --Labaran wasannin
 --Me ka sani
(GMT+08:00) 2008-02-18 17:04:20    
Kasar Sin za ta kafa tsarin ba da inshora ga harasar da ake yi daga gurbata muhalli

cri

Bayan haka Malam Bie Tao ya jaddada cewa, kafa tsarin ba da inshora ga masana'antu da ke sauke da nauyin gurbata muhalli bisa wuyansu, ba abin da ake nufi cewa, wai masana'antun da suka sami inshora za su iya gurbata muhalli yadda suka ga dama ba. Dalilin da ya sa haka shi ne domin yawan kudin da masana'antun ke biya ga kamfanonin inshora ya shafi yawan hasarar da ake yi daga wajen hadarin gurbata muhalli da suke yi. Idan wani masana'antu ya yi hadarin gurbata muhalli sosai, to, kudi mai yawa da yake biya wa kamfanonin ba da inshora zai zama babban nauyin da ba zai iya dauka ba. Bisa labarin da aka bayar, an ce, a shekarar nan, kasar Sin za ta yi gwajin ba da inshora ga hasarar da ake yi daga wajen gurbata muhalli domin wasu masana'antun man fetur da na sarrafa magunguna da sauransu wadanda ke gurbata muhalli cikin sauri. Babbar hukumar kiyaye muhalli ta kasar Sin za ta ba da kwarin gwiwa ga masana'antun da su sami inshora ga hasarar da ake yi daga wajen hadarinsu na gurbata muhalli.

Malam Dong Bo, mataimakin shugaban sashen ba da insharar dukiya na hukumar kula da harkokin inshora ta kasar Sin ya bayyana cewa, "kamfanin inshora yana la'akari da moriyarsa a fannin tattalin arziki cewa, idan hadarin gurbata muhalli ya sha auku a wani masana'antu, to, da farko kamfanin zai biya diyya ga hasarar da aka yi daga wajen hadarin. Ta haka za a tauye moriyarsa. Sabo da haka kafin aukuwar hadarin, kamfanin zai yi bincike a kan abubuwan da za su yiwu su gurbata muhalli a masana'antu. Idan ya gano abubuwan da za su kawo hadarin gurbata muhalli, to, zai sauke da nauyi bisa wuyansu na sanar da hukumomin kiyaye muhalli na kasar. Kamfanin inshora zai ki bayar da inshora ga masana'antun wadanda ba su kai ma'aunan kiyaye muhalli ba. Sa'an nan zai bayar da labarun da abin ya shafa ga hukumomin kiyaye muhalli."

Malam Dong Bo ya fayyace cewa, hukumar kula da harkokin inshora ta kasar Sin za ta hada kanta da babbar hukumar kiyaye muhalli ta kasar don sa kaimi ga aiwatar da aikin kafa doka kan nauyim da ake dauka na gurbata muhalli, sa'an nan za su bukaci kamfanonin insora da su ba da inshora iri na sabon salo. (Halilu)


1 2