Sin ciki da waje (chinaabc)Rediyon kasar SinSashen Hausa
China Radio International
Labarun gida
Labarun duniya
Labarun Siyasa
Labarun Tattalin Arziki
Labarun Al'adu
Labarun Wasanni
Sauran Labaru
Saurari labarai da dumi-duminsu da sauran shirye-shirye
more>>
[ Al'adu ]
 --Al'adun Sinawa
 --Kabilun kasar Sin
[ Bunkasuwa ]
 --Tattalin arziki
 --Bunkasuwar Sin
[ Yawon shakatawa ]
 --Yawo a kasar Sin
 --Wurare masu yawo
[ Ilmi, Lafiya ]
 --Fagen bincike
 --Kiwon lafiya
[ Wasanni ]
 --Labaran wasannin
 --Me ka sani
(GMT+08:00) 2008-02-18 17:04:20    
Kasar Sin za ta kafa tsarin ba da inshora ga harasar da ake yi daga gurbata muhalli

cri

A kwanakin baya, babbar hukumar kiyaye muhalli ta kasar Sin da hukumar kula da harkokin inshora ta kasar sun bayar da bayani, inda aka bayyana cewa, kasar Sin tana shirin kafa tsarin ba da inshora ga hararar da ake yi daga gurbata muhalli sannu a hankali. Nan gaba, manasa'antun kere-kere na kasar Sin za su sami inshora daga kamfanonin inshora a kan hasarar da take yi daga gurbata muhalli, kamfanonin inshora kuma za su biya diyya ga jama'ar wadanda hadarin gurbata muhalli ya rutsa da su. Wani jami'in babbar hukumar kiyaye muhalli ta kasar Sin ya bayyana cewa, kafa tsarin ba da inshora ga hasarar da ake yi daga wajen gurbata muhalli, zai ba da taimako wajen sa kaimi ga masana'antu da su rage fitar da abubuwa masu gurbata muhalli, kuma zai rage matsin da hukumomi ke sha wajen biya diyya ga wadanda hadarin gurbata muhalli ya rutsa da su.

An labarta cewa, yanzu kasar Sin ta riga ta shiga cikin lokacin da ake samu hadarurrukan gurbata muhalli masu yawa. Malam Bie Tao, mataimakin shugaban sashen kula da manufofi da dokoki na babbar hukumar kiyaye muhalli ta kasar Sin ya bayyana cewa, "ta hanyar kafa wannan tsari, idan wani masana'antu ya gurbata muhalli sosai ba zato ba tsammani, to, ba za a rufe shi ba sabo da hasarar da ta yi, haka kuma mutanen da hadarin gurbata muhalli ya rutsa da su su ma za su sami diyyar kudi cikin lokaci kamar yadda ya kamata. Sa'an nan za a kubutar da hukumomi daga nauyin da bai kamata su sauke a wuyansu ba. Sabo da haka a ganinmu, wannan tsari wani kyakkyawan tsari ne da za a kafa don masana'antu da mutanen da hadarin gurbata muhalli ya rutsa da su da kuma hukumomin da abin ya shafa za su sauke nauyi da ke bisa wuyansu kamar yadda ya kamata. "


1 2