Sin ciki da waje (chinaabc)Rediyon kasar SinSashen Hausa
China Radio International
Labarun gida
Labarun duniya
Labarun Siyasa
Labarun Tattalin Arziki
Labarun Al'adu
Labarun Wasanni
Sauran Labaru
Saurari labarai da dumi-duminsu da sauran shirye-shirye
more>>
[ Al'adu ]
 --Al'adun Sinawa
 --Kabilun kasar Sin
[ Bunkasuwa ]
 --Tattalin arziki
 --Bunkasuwar Sin
[ Yawon shakatawa ]
 --Yawo a kasar Sin
 --Wurare masu yawo
[ Ilmi, Lafiya ]
 --Fagen bincike
 --Kiwon lafiya
[ Wasanni ]
 --Labaran wasannin
 --Me ka sani
(GMT+08:00) 2008-02-05 21:37:28    
Afirka na dora muhimmanci a kan bunkasa makamashi tare kuma da yin tsiminsu

cri

A wajen bunkasa makamashin iska da na rana, ba shakka Afirka ta kudu ta zo ta farko a nahiyar Afirka gaba daya. Sa'an nan, Nijeriya ita ma tana kokarin bunkasa makamashin rana. Yanzu a duk fadin Nijeriya, akwai kamfanoni fiye da 60 da ke gudanar da harkokin makamashin rana, har ma an kafa kwamitin kula da makamashin rana, a yayin da suke kokarin nazarin makamashin rana da kuma bunkasa shi, suna kuma kokarin inganta hadin gwiwar da ke tsakaninsu da kasashen waje. Bayan haka, kasashen Kenya da Zambia su ma sun sanya bunkasa makamashin rana a cikin ajandarsu.

Masu sauraro, masana'antar samar da wutar lantarki da makamashin rana da muka ambata a farkon shirinmu, za ta kasance irinta na farko a kasar Masar, kuma ana sa ran cewa za ta iya taimakawa wajen sassauta karancin makamashi da Masar ke fama da shi. Ban da wannan, Masar tana kuma da fifiko wajen bunkasa wutar lantarki da karfin iska, kuma a hakika, Masar ta riga ta gina wata masana'antar bunkasa wutar lantarki da karfin ruwa a gabar yamma ta mashigin ruwa na Suez, lokacin da aka bi ta wurin cikin mota, ana iya hangen dimbin na'urorin samar da wutar lantarki da ake kira "wind mill". Ba shakka, kara gina masana'antun bunkasa wutar lantarki da karfin iska zai kara ciyar da Masar gaba a fannin yin amfani da sabbin makamashi.(Lubabatu)


1 2