Sin ciki da waje (chinaabc)Rediyon kasar SinSashen Hausa
China Radio International
Labarun gida
Labarun duniya
Labarun Siyasa
Labarun Tattalin Arziki
Labarun Al'adu
Labarun Wasanni
Sauran Labaru
Saurari labarai da dumi-duminsu da sauran shirye-shirye
more>>
[ Al'adu ]
 --Al'adun Sinawa
 --Kabilun kasar Sin
[ Bunkasuwa ]
 --Tattalin arziki
 --Bunkasuwar Sin
[ Yawon shakatawa ]
 --Yawo a kasar Sin
 --Wurare masu yawo
[ Ilmi, Lafiya ]
 --Fagen bincike
 --Kiwon lafiya
[ Wasanni ]
 --Labaran wasannin
 --Me ka sani
(GMT+08:00) 2008-02-05 21:37:28    
Afirka na dora muhimmanci a kan bunkasa makamashi tare kuma da yin tsiminsu

cri

A farkon wannan sabuwar shekarar da muke ciki, a hukunce ne Masar ta fara aiwatar da manyan shirye-shirye biyu na makamashi, daya shi ne bunkasa wutar lantarki da iska, dayan kuma shi ne samar da wutar lantarki da makamashin rana. A hakika dai, bayan Masar, kasashen Afirka da dama na kokarin neman sabbin makamashi da kuma bunkasa su.

Na farko, suna kokarin yin cikakken amfani da tsoffin albarkatun kasa da suke da shi. Alal misali, a wajen bunkasa wutar lantarki da karfin ruwa, bisa rahoton da asusun kula da halittun duniya ya bayar, an ce, Afirka na da karfin ruwa da zai iya samar da wutar lantarki kimanin KW miliyan 30, amma duk da haka, yanzu an bunkasa kashi 10% nasa ne kawai. Sabo da haka, kasashen Kamaru da Congo Kinshasa da Habasha da dai sauran kasashen da ke da arzikin albarkatun ruwa sun riga sun fara kokari, har ma sun sanya bunkasa karfin ruwa a wani muhimmin matsayin da ya zo daya da na neman sabbin makamashi. A yanzu haka dai, yawan wutar lantarki da tashoshin bunkasa wutar lantarki na kasashen uku ke samarwa ya kai kimanin KW miliyan 2.8, kuma sabbin tashoshin da ake ginawa na iya samar da wutar lantarki da yawansa ya kai KW miliyan 4.

Na biyu kuwa, kasashen Afirka na kokarin bunkasa makamashin da aka samu daga halittu, kuma kasar Senegal ta zo gaba a wannan fanni. A cewar shugaban kasar Senegal, "man da aka samu daga halittu zai iya tayar da wani sabon juyin juya hali a nahiyar Afirka." A kasar Senegal, an kafa hukumar musamman don nazarin makamashin da ake samu daga halittu da kuma makamashin da za a iya sabuntawa, kuma kasar ta yi koyi da kasar Brazil da sauransu, har ma manoman wasu lardunan kasar sun fara noman ciyayin da zai iya sauyawa zuwa alcohol. A sa'i daya, Senegal tana kuma shirin dasa itatuwan da za a iya tace man dizal na kadada 116 a gabashin kasar. Ban da wannan, sabo da makamashin da aka samu daga halittu ba za su lalata muhalli ba, shi ya sa kasashe da dama na yammacin Afirka suka gabatar da rahoton musamman, don ba da shawarar yin amfani da makamashin da aka samu daga halittu da kuma kiyaye muhalli.

Daga karshe, kasashen Afirka suna kuma neman makamashi daga iska da kuma rana. A cikin harshen Latin da kuma na Girika, "Afirka" na nufin wurin da ake shan rana sosai. Dimbin kasashen Afirka suna kan ikwaita ko kuma kusa da shi, inda ake shan rana sosai. A waje daya, Afirka na da Plato da dama, shi ya sa ana iya samun karfin iska sosai. Sabo da makamashin rana da na iska makamashi ne mai tsabta wanda ba zai kare ba, shi ya sa Afirka na da makoma mai kyau wajen yin amfani da makamashin rana da na iska.


1 2