Sin ciki da waje (chinaabc)Rediyon kasar SinSashen Hausa
China Radio International
Labarun gida
Labarun duniya
Labarun Siyasa
Labarun Tattalin Arziki
Labarun Al'adu
Labarun Wasanni
Sauran Labaru
Saurari labarai da dumi-duminsu da sauran shirye-shirye
more>>
[ Al'adu ]
 --Al'adun Sinawa
 --Kabilun kasar Sin
[ Bunkasuwa ]
 --Tattalin arziki
 --Bunkasuwar Sin
[ Yawon shakatawa ]
 --Yawo a kasar Sin
 --Wurare masu yawo
[ Ilmi, Lafiya ]
 --Fagen bincike
 --Kiwon lafiya
[ Wasanni ]
 --Labaran wasannin
 --Me ka sani
(GMT+08:00) 2008-02-05 15:24:02    
Kasar Sin ta tsara littafin ja-gora wajen sayen abubuwan kalaci don yara

cri

"yaran da shekarunsu ya kai 3 zuwa 5 da haihuwa, suna da kwarewa sosai wajen kwaikwayo, shi ya sa abubuwan da iyayensu da malamansu da kuma masu lura da su suke yi sun ba da tasiri sosai garesu. Alal misali, idan iyayensu sun gaya musu cewa, karas ba shi da dadin ci, to tabbas ne yaran ba za su ci ba. Sabo da haka ya kamata masu lura da yara su san ilmin kalaci da farko, ta yadda za su ja wa yara gora wajen cin wasu abubuwan kalaci masu gina jiki."

Haka kuma an labarta cewa, domin taimaka wa iyaye da yara wajen fahimtar abubuwan kalaci iri daban daban, da kuma zabarsu yadda ya kamata, an sanya hotunan kalaci a cikin littafin ja-gora. Zhang Bing, mataimakin shugaban ofishin ya gaya mana cewa:

"mun kasa abubuwan kalaci cikin manyan ire-ire goma a cikin littafin ja-gora. Yanzu mun riga mun tattara abubuwan kalaci iri iri fiye da 400, sa'an nan kuma mun dauki hotunansu, da kuma bayyana sinadarin gina jiki da ke cikinsu."

Bisa tushen sanya hotunan abubuwan kalaci, littafin ja-gora ya kasa abubuwan kalaci cikin rukunoni uku, wato "kalacin da ake iya yinsa kullum", da "kalacin da ake iya yinsa kadan", da kuma "kalacin da ake kayyade wajen yinsa". Ta haka, iyaye za su iya zabar abubuwan kalaci masu gina jiki ga yaransu. (Kande Gao)


1 2