Sin ciki da waje (chinaabc)Rediyon kasar SinSashen Hausa
China Radio International
Labarun gida
Labarun duniya
Labarun Siyasa
Labarun Tattalin Arziki
Labarun Al'adu
Labarun Wasanni
Sauran Labaru
Saurari labarai da dumi-duminsu da sauran shirye-shirye
more>>
[ Al'adu ]
 --Al'adun Sinawa
 --Kabilun kasar Sin
[ Bunkasuwa ]
 --Tattalin arziki
 --Bunkasuwar Sin
[ Yawon shakatawa ]
 --Yawo a kasar Sin
 --Wurare masu yawo
[ Ilmi, Lafiya ]
 --Fagen bincike
 --Kiwon lafiya
[ Wasanni ]
 --Labaran wasannin
 --Me ka sani
(GMT+08:00) 2008-02-05 15:24:02    
Kasar Sin ta tsara littafin ja-gora wajen sayen abubuwan kalaci don yara

cri

A cikin shekaru kusan goma da suka gabata, jimlar kudaden da aka kashe wajen sayen abubuwan kalaci ga yara tana ta samun karuwa, musamman ma jimlar ta samu saurin karuwa daga shekara ta 2000 zuwa shekara ta 2004. Bisa binciken musamman da ofishin kula da abubuwan gina jiki da ingacin abinci na cibiyar rigakafi da shawo kan cututtuka ta kasar Sin ya gudanar a shekara ta 2007 wajen kalacin da mazaunan kasar Sin suke yi, an ce, fiye da kashi 60 bisa dari da ke cikin yaran da shekarunsu ya kai 3 zuwa 17 da haihuwa suna yin kalaci a ko wace rana.

A 'yan shekarun nan da suka gabata, dimbin iyayen yara na kasar Sin suna ganin cewa, yin kalaci wata al'ada ce maras kyau. Amma kwararru sun nuna cewa, jama'ar Sin suna da kuskure wajen fahimtar kalaci, yin kalaci yana da amfani bisa wani matsayi. Madam Yu Dongmei mai digiri PHD ta ofishin kula da abubuwan gina jiki da kuma ingancin abinci ta bayyana cewa:

"a wani gefe, kalaci abu ne maras kyau, mai yiyuwa ne zai yi illa ga abincin da yara suke ci, kuma kila wasu yara ba za su iya samun isassun abubuwan gina jiki sakamakon kalaci ba, haka kuma wasu za su samu nauyin jiki fiye da kima. Amma a wani gefen daban, kalaci yana da amfani wajen sassauta yunwar da yara su kan ji tsakanin abincin safe da na rana da kuma na dare, ta yadda za a iya magance cin yawan abinci fiye da kima."

Bisa yin la'akari da halin sayen kalaci don yara da kasar Sin ke ciki yanzu, da kuma sa kaimi ga girman yara yadda ya kamata, kwararrun kasar Sin sun tsara littafin ja-gora wajen sayen abubuwan kalaci don yara bayan da suka gudanar da bincike da kuma koyon ka'idojin kasar Amurka da shiyyar HongKong ta kasar Sin a wannan fanni.

A cikin wannan littafin ja-gora, an kasa yara cikin rukunoni uku, wato yaran da shekarunsu ya kai 3 zuwa 5 da haihuwa, da wadanda shekarunsu ya kai 6 zuwa 12 da haihuwa, da kuma wadanda shekarunsu ya kai 13 zuwa 17 da haihuwa, sa'an nan kuma an ba da shawarwarin ja-gora na kimiyya da ake iya fahimta sosai. Madam Zhai Fengying, mataimakiyar shugaban ofishin kula da abubuwan gina jiki da ingancin abinci ta bayyana cewa, an bayar da shawarwarin musamman don yaran da ke cikin rukunoni daban daban. Kuma ta kara da cewa:


1 2