A ko ina a babban dutsen Huaguoshan, ana iya ganin kyawawan kananan birai, su ne masu gida na gaskiya a wannan babban dutse. Su kan janyo hankulan ko wane mutumin da ke ziyarar a wannan babban dutse. Wadannan birai suna wasa da juna, suna dudduba masu yawon shakatawa, wasu lokuta, su kan gaisar da masu yawon shakatawa, ba sa jin tsoron mutane ko kadan ba. Sa'an nan kuma, masu yawon shakatawa suna kaunar wadannan kyawawan birai kwarai.
A ko wace shekara, dimbin masu yawon shakatawa suna ta kawo wa babban dutsen Huaguoshan ziyara domin more idanunsu da gine-ginen al'adun mutane masu yawa da kuma kyan karkara. A shekaru da yawa da suka wuce, masu yawon shakatawa da ba a iya kidaya yawansu ba sun shiga wannan aljannar duniya tare da kyakkyawan burinsu. Ni'imtattun wurare masu nuna sigar musamman ta tatsuniya a babban dutsen Huaguoshan su kan burge ko wane mutum sosai. Malama Habibah Binti ta kawo wa babban dutsen Huaguoshan ziyara daga kasar Malaysia a karo na farko. A idonta, babban dutsen Huaguoshan ya burge ta sosai. Ta ce:
'
Ina ganin wurare masu matukar ni'ima a wajen. Yanayi kuma ya yi kyau. Na kuma ziyarci gine-ginen al'adun mutane da yawa. Na ji farin ciki saboda kawo wa wannan babban dutse ziyara.'
Ana iya samun tsire-tsire iri daban daban a babban dutsen Huaguoshan. Ana kuma iya ganin kyan karkara a nan. A duk shekara ana iya samun kayayyakin lambu da 'ya'yan itatuwa da kuma amfanin gona. A ciki kuma, wani irin ganyayen shayi mai suna Yunwucha ya yi suna sosai. Li Daoying, shugaban hukumar harkokin yawon shakatawa ta birnin Lianyungang ya yi karin bayani cewa, ganyayen shayin Yunwucha na zama a cikin gajimare da hazo a duk shekara, shi ya sa ake kiransu Yunwucha, wato ganyayen shayi da ke zama a gajimare da hazo. Li ya ce:
'Don me ingancin irin wannan ganyen shayi ya yi kyau kamar hakan? Dalilin shi ne domin akwai wata almarar cewa, a can da, mutane suna kiwon kaji da yawa a babban dutsen, bayan da suka jefa kwai a ko wace rana misalin karfe 10 da safe, wadannan kwayaye su kan bace. Ashe, wani maciji yake cin wadannan kwayaye. Shi ya sa mutane suka yi dabara suka nemi kama ta. Suka ajiye duwatsu a cikin kwayaye. Kashegari misalin karfe 10 da safe, macijin ya zo ya cinye wadannan kwayaye, daga baya, ya tashi, amma bai iya hawan ice ba. Ya ci irin wadannan ganyayen shayi na Yunwucha. Ta haka, duwatsun da ke cikinsa suka narke. Mutane suka gano cewa, wadannan ganyayen shayi na iya taimakawa wajen narke abinci.'
To, masu karatu, karshen shirinmu na yau ke nan, in kuna da dama, ya fi kyau ku ziyarci babban dutsen Huaguoshan da kanku da kuma shan shayin Yunwucha mai dadin sha. 1 2
|