Masu karatu, in kun karanta shahararren littafin gargajiya na kasar Sin mai suna 'Ziyara zuwa yamma, wato Tatsuniyoyin wani biri mai wayo da ake kira Sun Wukong', to, tabbas ne za ku tuna da wannan sarikin biri wai shi Sun Wukong, wanda ya yi kome da kome. Bisa wannan littafi, garin Sun Wukong shi ne wani babban dutse mai ban mamaki wato babban dutsen Huaguoshan. Lalle a birnin Lianyungang na lardin Jiangsu a gabashin kasar Sin, akwai wani babban dutse wai shi Huaguoshan. An ce, shi ne asalin babban dutse na Huaguoshan a cikin littafin 'Tatsuniyoyin wani biri mai wayo da ake kira Sun Wukong'.
Kamar yadda littafin 'Tatsuniyoyin wani biri mai wayo da ake kira Sun Wukong' ya fada, a babban dutsen Huaguoshan, yanayi ya yi kyau a duk shekara, kuma babban dutsen na da kyan gani sosai, shi ne aljanna a duniyarmu da ba a iya samun irinsa a sauran wurare ba.
Akwai muhimman wuraren yawon shakatawa fiye da 100 a babban dutsen Huaguoshan, da yawa daga cikinsu sun yi daidai da abubuwan da aka rubuta a cikin littafin 'Tatsuniyoyin wani biri mai wayo da ake kira Sun Wukong'. A cikinsu, kogon dutsen Shuiliandong ya fi shahara. Shen Hailing, mai jagorar masu yawon shakatawa a wannan babban dutse ta gaya mana cewa, wata almara game da wannan kogon dutse da ta bazu a wurin. Ta ce:
'An ce, Wu Cheng'en, wanda ya rubuta littafin 'Tatsuniyoyin wani biri mai wayo da ake kira Sun Wukong' ya rintsa a cikin wannan kogon dutse a yayin da yake yawo a babban dutsen domin neman ilhamar rubutu. Wasu birai sun duba abubuwan da ya rubuta, sun ce, wannan tsoho ya dade yana yawo a nan, amma bai ambaci mu birai ba, shi ya sa suka yayyaga wadannan takardu. Bayan da Wu ya farka, a maimakon littafinsa da takardu da sauran abubuwa, ya ga wasu kyawawan birai a gabansa. Bai yi fushi da su ba. Ya fara kaunarsu, shi ya sa ya tanadi wadannan birai a cikin littafinsa.'
1 2
|