Babban manaja Hiroshi Chono ya ci gaba da cewa, kamfaninsa ya lura da manufofin da gwamnatin kasar Sin ta gabatar game da tsimin makamashi da rage fitar da abubuwa masu gurbata muhalli, da samun ci gaba mai dorewa wajen bunkasa tattalin arziki ba tare da gurbata muhalli ba, bisa wadannan manufofi, birnin Tangshan ya sami manyan sauye-sauye. Yana ganin cewa, neman samun ci gaba mai dorewa ya riga ya zama ra'ayi daya da gamayyar kasa da kasa ta samu, kuma yana da muhimmanci sosai ga dukan kamfanoni. Ya ce, "na fara yin aiki a babban kamfanin kera kayayyakin gyara motoci na Aishin ne a shekarar 1972. Yau shekaru 35 ke nan da nake aiki a kamfanin, na fahimci muhimmancin ra'ayin nan ga ma'aikatan kamfani. Akwai abubuwa masu muhimmanci biyu da kamfanoni ke yi wajen neman samun ci gaba mai dorewa, daya shi ne su sarrafa kayayyaki da ke samun karbuwa daga wajen masu saya, na biyu kuma shi ne, su sami wata hanyar da suke bi wajen samun ci gaba mai dorewa kuma ba tare da gurbata muahlli ba.
Malam Hiroshi Chono yana fatan kamfaninsa zai sami ci gaba mai dorewa tare da birnin Tangshan na kasar Sin, kuma su sami kyakkyawar makomarsu tare. (Halilu) 1 2
|