Sin ciki da waje (chinaabc)Rediyon kasar SinSashen Hausa
China Radio International
Labarun gida
Labarun duniya
Labarun Siyasa
Labarun Tattalin Arziki
Labarun Al'adu
Labarun Wasanni
Sauran Labaru
Saurari labarai da dumi-duminsu da sauran shirye-shirye
more>>
[ Al'adu ]
 --Al'adun Sinawa
 --Kabilun kasar Sin
[ Bunkasuwa ]
 --Tattalin arziki
 --Bunkasuwar Sin
[ Yawon shakatawa ]
 --Yawo a kasar Sin
 --Wurare masu yawo
[ Ilmi, Lafiya ]
 --Fagen bincike
 --Kiwon lafiya
[ Wasanni ]
 --Labaran wasannin
 --Me ka sani
(GMT+08:00) 2008-02-04 15:44:47    
Baban manaja Hiroshi Chono dan kasar Japan na sha'awar kiyaye muhalli a kasar Sin

cri

Babban kamfanin kera kayayyakin gyara motoci na Aisin na kasar Japan yana daya daga cikin manyan kamfanonin duniya dari biyar. A shekarar 2005, wannan babban kamfani ya zuba kudin jari da yawansu ya kai dalar Amurka miliyan 99.5 don kafa reshenta a birnin Tangshan na lardin Hebei na kasar Sin. Malam Hiroshi Chono, dan kasar Japan ya zama babban manajan reshen kamfanin.

A cikin shekaru biyu da suka wuce bayan da aka kafa reshen kamfanin, a sakamakon ci gaban da kasar Sin ta samu wajen bunkasa masana'antun kera motoci cikin sauri, reshen babban kamfanin kera kayayyakin gyara motoci na Aisin a birnin Tangshan shi ma ya sami bunkasuwa cikin sauri sosai. A cikin shekara daya da ta gabata, yawan ma'aikata da ya dauka ya karu da ninki biyar, ya zuwa karshen watan Oktoba da ya wuce, yawan kudin da ya samu daga wajen sayar da kayayyakinsa ya riga ya kai kudin Sin Renminbi Yuan miliyan 30.

Amma yayin da reshen kamfanin ke bunkasa harkokinsa, yana mai da hankali sosai ga kiyaye muhalli. Babban majana Hiroshi Ghono ya bayyana cewa, "wata manufar da kamfaninsa ke bi ko da yaushe ita ce kiyaye muhalli da kyau, yayin da yake sarrafa kayayyaki. Bisa wannan manufar, muka tsara "ka'idojin kiyaye muhalli" domin reshen babban kamfanin kera kayayyakin gyara motoci na Aisin a birnin Tangshan. Yanzu, babban kamfanin yana da rassansa 35 zuwa 40 a wurare daban daban na duniya, zuwa shekarar 2008, duk wadannan rassansa za su sami amincewa daga wajen tsarin kiyaye muhalli da ake kira ISO14001. Reshenmu ma mun mayar da martani ga kiran da babban kamfaninmu ya yi, za mu nemi samun amincewa daga wajen wannan tsarin."

Bayan da aka tsara "ka'idojin kiyaye muhalli", an buga wadannan ka'idojin a kan kananan katuna wadanda girmansu ta yi daidai da katin wurin aiki, ta yadda dukan ma'aikatan kamfanin za su fahimci wadannan ka'idojin kiyaye muhalli. A cikin wokusho na kamfanin, an ajiye akwatunan juji masu launuka iri daban daban don tattara juyi iri-iri da za a iya sake yin amfani da su. Da babban majana Hiroshi Chono ya tabo magana a kan wannan, sai ya bayyana cewa, ya kamata, a yi duk abubuwa da ake iya yi wajen tsimin makamashi da kiyaye muhalli a cikin zaman rayuwa da aiki. Ya kara da cewa, "kamata ya yi, a mai da hankali ga samun daidaituwa a tsakanin zamantakewar al'umma da halitta. Kamfaninmu yana amfani da danyun kayayyaki masu yawa da ake samu daga halitta don samar da kayayyaki, ta haka ana lalata halitta a wasu fannoni. Sabo da haka bayan da muka sarrafa kayayyakinmu, muna samar da su ga jama'a don kara daga matsayin zaman rayuwarsu ciki har da ma'aikatanmu, sa'an nan mu yi kokari wajen kiyaye halitta."


1 2