Sin ciki da waje (chinaabc)Rediyon kasar SinSashen Hausa
China Radio International
Labarun gida
Labarun duniya
Labarun Siyasa
Labarun Tattalin Arziki
Labarun Al'adu
Labarun Wasanni
Sauran Labaru
Saurari labarai da dumi-duminsu da sauran shirye-shirye
more>>
[ Al'adu ]
 --Al'adun Sinawa
 --Kabilun kasar Sin
[ Bunkasuwa ]
 --Tattalin arziki
 --Bunkasuwar Sin
[ Yawon shakatawa ]
 --Yawo a kasar Sin
 --Wurare masu yawo
[ Ilmi, Lafiya ]
 --Fagen bincike
 --Kiwon lafiya
[ Wasanni ]
 --Labaran wasannin
 --Me ka sani
(GMT+08:00) 2008-02-01 14:19:44    
Shin ko za a iya samun kwararan hadin gwiwa tsakanin sojojin kasar Amurika da dakarun wuri na Iraki

cri

Wani rahoto da ma'aikatar harkokin gida ta Iraki ta gabatar na nuna cewa, mutane kalilan ne aka kashe su a watan Disamba na shekarar da ta gabata sakamakon tashe-tashen hankula ; Ban da wannan kuma, an samu raguwar hare-haren ta'addanci da kashi 70 cikin kashi 100 daga kungiyar Al Qaeda ; Kazlika, an rushe kashi 75 cikin kashi 100 bisa yawan tashoshin internet na cikin yankin kasar Iraki. Sojojin Amurka sun ce, lallai kungiyoyin wayewar kai na Iraki sun taka muhimmiyar rawa wajen kyautata yanayin tsaro na kasar.

Amma duk da haka, Hafsan soji Brown ba zai iya sa ran alheri ga lamarin ba domin ya ga tilas ne ya rage yawan albashi da yaken biya wa 'yan kungiyoyin wayewar kai. Bisa abubuwan da aka tanada game da sojojin Amurka, dukkan hafsoshin soji na kasar a Iraki suna da ikon ware wasu kudade wajen daidaita matsalolin ba zata ; Amma wani labari da aka samu baya-bayan nan na nuna cewa, kila gwamnatin Amurka za ta tsuke bakin aljihunta wajen yin kasafin kudi da za a kashe a kasar Iraki. Game da wannan dai, hafsoshin soji da yawa na kasar a Iraki sun rasa abin da za su yi, a cewarsu, matukar gwamnatin Amurka ta yi haka, to hadin gwiwa dake tsakaninsu da shugabannin kabilu na Iraki,wanda suka kwashe watanni da dama suna yi zai bi ruwa ! Mr. Brown ya kuma fadi cewa, abin da ya fi bayyana damuwarsa a kai shi ne, da zarar suka kasa samun isasshen kudi da suke yin amfani da su wajen sa kaimi ga yin hadin gwiwa, to labuddah ba za a iya samun kyakkyawan tsaro a wannan kasa ba.

A hannu daya kuma, gwamnatin Iraki da kuma wasu fararen hula na kasar suna da nasu ra'ayoyi kan yadda sojojin kasar Amurka suke bada kudi domin samun hadin gwiwa daga dakarun wuri na kasar. Gwamnatin Iraki ta bayyana damuwarta cewa, idan an kori kungiyar Al-Qaeda daga kasar, to mai yiwuwa ne dakarun wuri na kasar za su mayar da gwamnatin kasar a mashin gaba da kuma sake sanya kasar cikin halin rudami. ( Sani Wang )


1 2