Aminai 'yan Afrika, ko kuna sane da cewa, an samu raguwar yawan matsalolin nuna karfin tuwo a cikin yankin kasar Iraki a wasu lokutan da suka gabata duk bisa taimakon da dakarun wuri na Iraki suka bai wa sojojin kasar Amurka a wanann kasa gwargwadon iyawa. Amma, ko wadannan dakaru za su iya ci gaba da sadaukar da ransu domin sojojin Amurka bayan da gwamnatin kasar Amurka ta tsuke bakin aljihunta a wannan fanni ?
Sanin kowa ne, sojojin kasar Amurka ba su samu cikakken tsaro ko kwana daya ba tun bayan da suka mamaye kasar ta Iraki. Domin kubatar da kansu daga halin kaka-ni-ka-yi, sojojin Amurka sun fito da wata dabara dake cewa ' Barin mutanen Iraki su yi yakin su-ya-su',wato ke nan a wasu wuraren dake fama da tashe-tashen hankula na kasar Iraki, sojojin Amurka su bada kyautar kudi ga dakaru 'yan Sunni da ba na gwamnati ba don taimaka wa sojojin na kasar Amurka da kuma gwamnatin Iraki wajen dakile 'yan kungiyar Al-Qaeda. Kafofin yada labarai na Iraki suna kiran wadannan kungiyoyin dakaru a kan cewa ' Kungiyoyin Wayewar Kai' yayin da sojojin Amurka suke kiransu ' mutane dake shafar fa'idar wuri'. An labarta cewa, yanzu akwai kungiyoyi kimanin 300 irinsu wadanda ke da mambobi kimanin 80,000 a kasar Iraki, kuma mutane da yawa dake cikinsu tsoffin dakaru ne da ba sa ga maciji da kasar Amurka har ma da gwamnatin Iraki.
Wani hafsan sojojin Amurka a Iraki mai suna Joy Brown ya bayyana cewa, jim kadan bayan da sojojin rundunarsa suka isa wani wuri dake kusa da kudancin birnin Bagadaza, sai suka gano boma-bomai 50 cikin kwana daya kawai, wadanda aka dasa su a gefunan hanyoyin mota, ko ma suka yi fadace-fadace tare da wasu dakaru sau biyu ko uku cikin kwana guda. Amma yanzu ya biya kudi ga kungiyoyin wayewar kai guda 9 na wurin don su tura 'yan kungiyoyinsu 300 zuwa tashoshin bincike guda 10 yayin da suke yin sintiri cikin sa'o'i 24 a wuraren dake kusa da makarantu da kuma asibitoci da dai sauran muhimman hanyoyi. Hakan ya bada tabbaci ga samun kyawawan tsaro da oda. A ganin hafsan soji Brown, da a ce sun yi fadace-fadace tare da sauran mutane, gwamma a ce su samar wa wadannan mutane aikin yi.
1 2
|