Sin ciki da waje (chinaabc)Rediyon kasar SinSashen Hausa
China Radio International
Labarun gida
Labarun duniya
Labarun Siyasa
Labarun Tattalin Arziki
Labarun Al'adu
Labarun Wasanni
Sauran Labaru
Saurari labarai da dumi-duminsu da sauran shirye-shirye
more>>
[ Al'adu ]
 --Al'adun Sinawa
 --Kabilun kasar Sin
[ Bunkasuwa ]
 --Tattalin arziki
 --Bunkasuwar Sin
[ Yawon shakatawa ]
 --Yawo a kasar Sin
 --Wurare masu yawo
[ Ilmi, Lafiya ]
 --Fagen bincike
 --Kiwon lafiya
[ Wasanni ]
 --Labaran wasannin
 --Me ka sani
(GMT+08:00) 2008-01-28 19:42:35    
Kasar Sin na namijin kokari domin tabbatar da isasshen kwal da wutar lantarki da man fetur

cri

Baya ga hanyar mota, a kwanan baya, ma'aikatar kula da hanyar dogo ta kasar Sin ta ba da umurci cikin gaggawa domin tabbatar da yin sufurin wutar lantarki da kwal.

Bugu da kari kuma, a ran 28 ga wata, a gun taron manema labaru da aka yi, Zhu Hongren, mataimakin shugaban sashen kula da gudanar da harkokin tattalin arziki na kwamitin yin gyare-gyare da raya kasar Sin ya jaddada cewa, a halin yanzu, saboda an fuskanci karancin wutar lantarki, shi ya sa tilas ne a bi ka'idar mayar da mutane a gaba da koma, haka kuma, a mayar da tabbatar da bai wa fararen hula wutar lantarki a gaba da kome.

Kazalika kuma, hukumar harkokin yanayi ta kasar Sin ta yi karin bayani cewa, a mako mai zuwa, za a ci gaba da yin ruwan sama da kankara mai laushi a yankunan tsakiya da gabashin kasar Sin. A kwanan baya, wannan hukuma ta riga ta aika da kungiyoyin kwararru zuwa lardunan da abin ya shafa domin jagorantar yaki da bala'i. Sa'an nan kuma, hukumomin harkokin yanayi na kasar Sin sun yi amfani da fasahohin zamani domin yin hasashe kan yanayi a nan gaba ba da dadewa ba.(Tasallah)


1 2