Sin ciki da waje (chinaabc)Rediyon kasar SinSashen Hausa
China Radio International
Labarun gida
Labarun duniya
Labarun Siyasa
Labarun Tattalin Arziki
Labarun Al'adu
Labarun Wasanni
Sauran Labaru
Saurari labarai da dumi-duminsu da sauran shirye-shirye
more>>
[ Al'adu ]
 --Al'adun Sinawa
 --Kabilun kasar Sin
[ Bunkasuwa ]
 --Tattalin arziki
 --Bunkasuwar Sin
[ Yawon shakatawa ]
 --Yawo a kasar Sin
 --Wurare masu yawo
[ Ilmi, Lafiya ]
 --Fagen bincike
 --Kiwon lafiya
[ Wasanni ]
 --Labaran wasannin
 --Me ka sani
(GMT+08:00) 2008-01-28 19:42:35    
Kasar Sin na namijin kokari domin tabbatar da isasshen kwal da wutar lantarki da man fetur

cri

Saboda kasar Sin tana fuskantar mummunar matsala wajen samar da isasshen kwal da wutar lantarki da man futer da yin sufurinsu cikin kwanciyar hankali a sakamakon bala'un ruwan sama da kankara mai laushi da kankara da aka samu a wurare masu fadi na kasar Sin a kwanan baya, shi ya sa a ran 27 ga wata, ta wayar tarho da talibijin majalisar gudanarwa ta kasar Sin ta shirya taron ayyukan tabbatar da isasshen kwal da wutar lantarki da man fetur da yin sufurinsu cikin kwanciyar hankali, inda firayim minista Wen Jiabao na kasar Sin ya jaddada a yi iyakacin kokari domin tabbatar da isasshen kwal da wutar lantarki da man fetur da yin sufurinsu cikin kwanciyar hankali. A halin yanzu, hukumomin kasar Sin da abin ya shafa da kananan hukumomin wurare daban daban na kasar Sin suna daukar matakai domin tabbatar da isasshen kwal da wutar lantarki da man fetur da yin sufurinsu cikin kwanciyar hankali cikin himma.

A lardin Jiangxi da ak fi shan wahalar kankara mai laushi a yankin tsakiyar kasar Sin, saboda an datse hanyoyi, shi ya sa ake gamuwa da matsalar rashin isasshen kwal da man fetur a yawancin wurare na wannan lardi. 'Yan sanda masu kula da zirga-zirga da 'yan sanda da sojojin kashe wuta da ma'aikata masu kula da harkokin hanya na wuraren suna hada kansu domin taimakawa ayarin motoci masu jigilar man fetur da kwal. Hu Lin, mataimakin shugaban sashen harkokin zirga-zirga na hukumar lardin Jiangxi ya gaya wa manema labaru cewa,'Muna gaggauta yin gyara kan dukkan manyan hanyoyi a lardinmu na Jiangxi, muna kuma gaggauta sake bude su da kuma kau da kankara a kansu. Da farko dai, mun aika da mutane fiye da dubu 10 domin tabbatar da zirga-zirga a kan hanyoyi yadda ya kamata. Kuma mun rarraba dubban 'yan sanda da sojojin kashe gobara a muhimman gadoji da gangara domin ba da agaji da kuma kiyaye zirga-zirga cikin kwanciyar hankali. Sa'an nan kuma, saboda mun fi fuskantar matsalar kankara, a maimakon kankara mai laushi a arewa, shi ya sa muka tura manyan injuna domin taimakawa mutane. Mun kuma ba da fifiko ga motoci masu daukar muhimman kayayyaki da kayayyakin masarufi, haka kuma, mun yafe wa masu daukar amfanin gona kudin amfani da hanyoyi.'

Kazalika kuma, a kwanan baya, ma'aikatar zirga-zirga ta kasar Sin ta kira taron harkokin zirga-zirga na kasar ta wayar tarho da talibijin, inda ta bukaci hukumomin harkokin zirga-zirga na wurare daban daban na kasar da su yi namijin kokari wajen yin sufurin wutar lantarki da kwal da sauran muhimman kayayyaki a manyan hanyoyi. Dangane da rashin isasshen wutar lantarki da kwal a yanzu, wannan ma'aikata ta kuma dakatar da yin sufuri zuwa ketare. Dai Dongchang, shugaban sashen kula da hanyoyin mota na ma'aikatar zirga-zirga ta kasar Sin ya ce,'Ba za a bata lokaci ko kadan ba, sai nan da nan a ba da fifiko wajen aza wa jiragen ruwa kaya da sauke kaya a gaba da saura. Sa'an nan kuma, ko kusa ba a yarda da ganin cewa, za a gamu da matsalar yin sufurin wutar lantarki da kwal a sakamakon ba a gudanar da ayyukan hanyoyin mota da na jiragen ruwa yadda ya kamata ba.'

1 2