Sin ciki da waje (chinaabc)Rediyon kasar SinSashen Hausa
China Radio International
Labarun gida
Labarun duniya
Labarun Siyasa
Labarun Tattalin Arziki
Labarun Al'adu
Labarun Wasanni
Sauran Labaru
Saurari labarai da dumi-duminsu da sauran shirye-shirye
more>>
[ Al'adu ]
 --Al'adun Sinawa
 --Kabilun kasar Sin
[ Bunkasuwa ]
 --Tattalin arziki
 --Bunkasuwar Sin
[ Yawon shakatawa ]
 --Yawo a kasar Sin
 --Wurare masu yawo
[ Ilmi, Lafiya ]
 --Fagen bincike
 --Kiwon lafiya
[ Wasanni ]
 --Labaran wasannin
 --Me ka sani
(GMT+08:00) 2008-01-25 16:32:12    
Gasar wasannin Olympics na kusanto wa farar hula na kasar Sin a shekarar 2007

cri

Madam Cao Fang, wata malama ce mai aikin sa kai dake koyar da harshen Turanci a wata unguwar Beijing. Ta fada wa wakilinmu cewa, yanzu akwai darurruwan malamai masu aikin sa kai a nan Beijing, wadanda dukansu dalibai ne masu jin harshen Turanci. Sa'annan ta ce, ko da yake akasarin masu koyon Turanci tsofaffi ne, amma suna koyo cikin himma da kwazo. Wata tsohuwa Hu daya daga cikinsu, yanzu ta riga ta rike wasu magangaun harshen Turanci. 'Beijing Belongs to you ; Beijing belongs to me; Beijing belongs to everyone. Welcome to Beijing.'

Karatowar gasar wasannin Olympics ba ma kawai ta cimma burin Sinnawa na shiga cikin harkokin wasannin Olympics ba, har ma ta canza rayuwar wasu mutane. Madam Zhang Jianshu tana daya daga cikinsu. Madam Zhang mai shekaru 47 da haihuwa, wata ma'aikaciya ce da ta sauka daga gurbin aikinta a birnin Kai Feng na lardin Henan dake tsakiyar kasar Sin. Yanzu ta kafa wata ma'aikatar yin surfani bayan da ta sake raya sana'a cikin cin gashin kai. Abun farin ciki shi ne ta samu iznin samar da hajjoji irin na musamman na wasannin Olympics na Beijing. ( Sani Wang )


1 2