Aminai masu sauraro, ko kuna sane da cewa, wata kalmar da Sinawa suka sha fadi a cikin zaman rayuwarsu da kuma aikinsu a shekarar bara, ita ce 'wasannin Olympics'. Ga gasar wasannin Olympics ta Beijing na karatowa. A cikin shirinmu na yau dai, bari mu dan gutsura muku yadda jama'ar kasar Sin suke samun manyan sauye-sauye a cikin zaman rayuwarsu yayin da suke share fagen wannan gagarumar gasa.
Akwai wata tsohuwa mai shekaru 103 da haihuwa a nan birnin Beijing. Sunanta Cao Zuozheng. Yanzu tana lafiya kalau saboda tana mai sha'awar wasan motsa jiki. Wannan tsohuwa ta yi farin ciki matuka da ganin cewa za a gudanar da gasar wasannin Olympics a Beijing wato garinta. Ta fada wa wakilinmu cewa, ba ma kawai za ta yi kallon gasanni ba, har ma tana kokarin tabbatar da kyakkyawan burinta. Tana mai cewa:
' Lallai ina so in zama wata mai daukar wutar yula ta wasannin Olympics domin neman daukaka kwarjinin kasar mahaifata'.
Burin tsohowa Cao Zuozheng ya samo asali ne tun tuni a lokacin da ake gudanar da bikin mika wutar yula ta gasar wasannin Olympics ta Aden a shekarar 2004 a nan birnin Beijing. A wancan lokaci dai, shekarunsta ya riga ya kai 100 da haihuwa. Amma duk da haka, ta je kallon mika wutar yula ko da yake ana zafi ainun, ta kuma dauka hoto tare da masu daukar wutar yula. A wannan lokaci, tsohuwa Cao ta yi tunanin cewa yaya ne za ta iya shiga harkokin gasar wasannin Olympics? A karshe dai, ta dau aniyar zama mai daukar wutar yula. 'Yan iyalinta sun fahimta kuma sun bada kwarin gwiwa ga wannan tsohuwa wajen neman tabbatar da burinta. 'Yan iyalinta sun kuma furta cewa, domin cimma burinta, tsohuwa Cao takan yi yawo a kowace rana. Jim kadan bayan da aka yi shelar gudanar da aikin karbar masu daukar wutar yula ta gasar wasannin Olympics ta Beijing, sai ta zo ta farko wajen gabatar da rokonta. Ta ce, idan ta dauki wutar yula kan titi, to aminai daga duk duniya za su iya ganin wata tsohuwa ta tsohon karni a Beijing da kuma sauye-sauyen zaman rayuwar Sinawa.
Kamar yadda tsohuwa Cao Zuozheng take, Sinawa masu tarin yawa su ma suna da nasu burin shiga cikin harkokin wasannin Olympics. Wata daliba mai suna Liang Chen daga Jami'ar zirga-zirgar sararin samaniya ta Beijing ta yi alfaharin zama mai daukar wutar yula. Ta fada wa wakilinmu cewa: 'Har kullum nakan mai da hankali sosai kan labarun wasannin Olympics, musamman ma kan masu daukar wutar yula. Ina mai sha'awar sanya irin zoben roba a wuyan hannuna da kuma irin tufa mai launin oringe da aka rubuta babbakun ' Baijing na yin sa'a' a kai'.
Jama'a masu sauraro, ko da yake mutane kalilan ne suka zama masu aikin sa kai domin gasar wasannin Olympics ta Beijing, amma Sinawa masu tarin yawa na kasar Sin suna bin salonsu na kansu domin nuna goyon baya ga gudanar da gasar wasannin Olympics a kasarsu da kuma gwada irin wannan gasa mafi sha'awa a duniya.
1 2
|