Sin ciki da waje (chinaabc)Rediyon kasar SinSashen Hausa
China Radio International
Labarun gida
Labarun duniya
Labarun Siyasa
Labarun Tattalin Arziki
Labarun Al'adu
Labarun Wasanni
Sauran Labaru
Saurari labarai da dumi-duminsu da sauran shirye-shirye
more>>
[ Al'adu ]
 --Al'adun Sinawa
 --Kabilun kasar Sin
[ Bunkasuwa ]
 --Tattalin arziki
 --Bunkasuwar Sin
[ Yawon shakatawa ]
 --Yawo a kasar Sin
 --Wurare masu yawo
[ Ilmi, Lafiya ]
 --Fagen bincike
 --Kiwon lafiya
[ Wasanni ]
 --Labaran wasannin
 --Me ka sani
(GMT+08:00) 2008-01-23 16:12:13    
Birnin Anshun, kyakkyawan wuri a yammacin kasar Sin

cri

Baya ga kyan karkara, yana kasancewa da al'ada ta musamman a Anshun, wato al'adar yankin Tunbao. Al'adar yankin Tunbao wato irin al'ada ce da ta sha bamban da saura, kuma an same ta ne a wurin tarihi na aikin soja na zamanin da na kasar Sin. Ko da yake shekaru fiye da dari 6 da suka wuce, amma har zuwa yanzu, mazaunan yankin Tunbao suna kiyaye al'adun gargajiya irin na zamanin daular Ming na kasar Sin, kuma suka sanya tufafi irin na zamanin daualar Ming, suna yin harkokin nishadi da kuma gina gidaje bisa hanyar da aka bi a zamanin daular Ming.

Yanzu ana kiyaye al'adar yankin Tunbao yadda ya kamata. Malam Chen ya ci gaba da cewa:

'Yanzu al'adar yankin Tunbao tana kasancewa a karkashin kiyayewar gwamnatin kasar. Mun kuma yi shirin shigar da ita cikin jerin wuraren tarihi na duniya na hukumar UNESCO cikin sauri.'

Saboda kyautatuwar sufuri da gidajen kwana, mutane da yawa suna ta kai wa Anshun ziyara. Masu sauraro, kada ku yi ta jira, ya fi kyau ku kai wa Anshun ziyara cikin sauri.


1 2