In an tabo magana kan birnin Anshun, mai yiwuwa ne masu sauraronmu ba ku da masaniya, amma in an tabo magana kan babbar magangarar ruwa ta Huangguoshu, dimbi daga cikinku za ku ce, ashe, mun san sunanta tun can da. Babbar magangarar ruwa ta Huangguoshu da ta fi girma a duniya a matsayin jerin ruwan da ke gangarowa tana cikin birnin Anshun.
Birnin Anshun yana cikin kudu maso yammacin kasar Sin, shi ne wani muhimmin birni a lardin Guizhou na kasar Sin. Yana cikin yankin da ya raba manyan koguna 2 na kasar Sin, wato kogin Yangtse da bangaren sama na kogin Zhujiang. Fadinsa ya kai kusan murabba'in kilomita dubu 10.
An mayar da Anshun birni mafi kyan gani a yammacin kasar Sin, saboda ana iya ganin ni'imtattun wurare masu tsarin yanayin kasa na Karst. Fadin irin wadannan wurare ya kai misalin kashi 70 cikin kashi dari bisa na dukkan birnin. Malam Chen Haifeng, sakataren kwamitin jam'iyyar kwaminis ta kasar Sin na birnin Anshun ya gaya mana cewa, mutane da yawa sun san birnin Guilin na kasar Sin, kuma birnin Guilin ya shahara ne bisa wurare masu tsarin yanayin kasa na Karst, amma a zahiri kuma, kyawawan wurare masu tsarin yanayin kasa na Karst a Anshun sun yi daidai da na Guilin.
'Wurare masu tsarin yanayin kasa na Karst a Anshun sun fi nuna sigar musamman na irin wannan tsarin yanayin kasa na musamman, in an kwatanta su da na Guilin, wato akwai duwatsu da yawa a nan. Sa'an nan kuma, akwai kogunan dutse da kuma ruwan da ke gangarowa masu tarin yawa a wurin. Babbar magangarar ruwa ta Huangguoshu na matsayin wani wakilinsu ne kawai. In an kai wa Anshun ziyara, a ko ina za a iya ganin ruwan da ke gangarowa da kuma kogunan dutse.'
Babbar magangarar ruwa ta Huangguoshu wani jerin ruwan da ke gangarowa ne mai girma sosai. An mayar da babbar magangarar ruwa ta Huangguoshu a cibiyar wannan jerin ruwan da ke gangarowa, wadda tsayinta ya kai misalin mita 77.8, kuma fadinta ya kai misalin 101. Akwai sauran kyawawan manyan magangarar ruwa manya da kanana guda 18 da suka sha bamban da juna a wajen. Dukan wadannan magangarar ruwa guda 19 sun zama iyalin ruwan da ke gangarowa. Babban zauren hukumar kula da matsayin bajinta ta Guinness ya mayar da babbar magangarar ruwa ta Huangguoshu a matsayin jerin ruwan da ke gangarowa mafi girma a duniya. Kazalika kuma, wannan babbar magangarar ruwa ita ce magangarar ruwa kacal a duniya da ake iya jin dadin kallonta daga sama da kasa, da gaba da ita da baya da ita, da kuma daga hagu da dama, haka kuma, akwai wani kogon dutse a cikinta, shi ya sa mutane suke iya ratsa wannan babbar magangarar ruwa tare da jin mamaki cewa, ita ce ikon Allah.
A watanni da dama da suka wuce, hukumar kula da harkokin yawon shakatawa ta kasasr Sin ta gabatar da wuraren yawon shakatawa na matsayin gwamnati a matsayin 5A guda 66 a rukuni na farko. Wurin yawon shakatawa na matsayin 5A wurin yawon shakatawa ne mafi kyan gani a kasar Sin. Magangarar ruwa ta Huangguoshu da wani wurin yawon shakatawa daban da ke kusa da ita suna cikin wannan takardar sunaye. Game da wannan, malam Chen ya ce:
'Akwai birane 2 kawai a cikin dukkan biranen kasar Sin, wadanda suke da wurare masu kyau na yawon shakatawa a matsayin 5A guda 2 ko fiye bisa wannan takardar sunaye. Birnin Beijing yana da irin wannan wurin yawon shakatawa 3, sa'an nan kuma, birninmu na Anshun yana da guda 2.'
1 2
|