Sin ciki da waje (chinaabc)Rediyon kasar SinSashen Hausa
China Radio International
Labarun gida
Labarun duniya
Labarun Siyasa
Labarun Tattalin Arziki
Labarun Al'adu
Labarun Wasanni
Sauran Labaru
Saurari labarai da dumi-duminsu da sauran shirye-shirye
more>>
[ Al'adu ]
 --Al'adun Sinawa
 --Kabilun kasar Sin
[ Bunkasuwa ]
 --Tattalin arziki
 --Bunkasuwar Sin
[ Yawon shakatawa ]
 --Yawo a kasar Sin
 --Wurare masu yawo
[ Ilmi, Lafiya ]
 --Fagen bincike
 --Kiwon lafiya
[ Wasanni ]
 --Labaran wasannin
 --Me ka sani
(GMT+08:00) 2008-01-23 09:33:27    
Tarzomar Kenya ta kawo babbar illa ga tattalin arzikin yankin Gabashin Afirka

cri

Don fitar da kasashe marasa mafitan teku daga halin yanzu, wato suna dogara da tashar jiragen ruwa ta Mombasa kwarai, kasashen gabashin Afirka sun mai da hankulansu kan tashar jiragen ruwa da ke Dares Salaam na Tanzania, suna fatan za su fito da sabbin hanyoyin sufuri. A makon jiya, gwamnatocin Uganda da Ruwanda sun aika da tawagarsu zuwa Tanzania domin yin tattaunawa da gwamnatin Tanzania kan yiwuwar yin jigilar abubuwa ta tashar jiragen ruwa ta Dares Salaam. Amma saboda ba a iya shigowa da fitar da kayayyaki masu yawa a tashar jiragen ruwa ta Dares Salaam ba, haka kuma, ba a kasancewa da hanyoyi masu inganci a tsakanin Tanzania da kasashe masu makwabtaka da ita, shi ya sa za a bukatar tattauna yiwuwar aiwatar da wannan shiri.

Ko da yake shugaba John Agyekum Kufuor na kasar Ghana, wanda kuma yake shugabantar kungiyar tarayyar Afirka a wannan gami, da tsoffin shugabanni 4 na kasashen Afirka da kuma Jendayi Frazer, mai ba da taimako ga sakatariyar harkokin waje ta kasar Amurka sun shiga tsakina, amma ba a sassauta rikicin siyasa a Kenya ba tukuna. Kwararru suna ganin cewa, in ba a warware rikicin siyasa a Kenya cikin sauri ba, za a kara raunana karfin zuciyar masu zuba jari baki, ta haka da kyar za a kidaya asarar da za a samu ta fuskar tattalin arziki a yankin gabashin Afirka.(Tasallah)


1 2