Sin ciki da waje (chinaabc)Rediyon kasar SinSashen Hausa
China Radio International
Labarun gida
Labarun duniya
Labarun Siyasa
Labarun Tattalin Arziki
Labarun Al'adu
Labarun Wasanni
Sauran Labaru
Saurari labarai da dumi-duminsu da sauran shirye-shirye
more>>
[ Al'adu ]
 --Al'adun Sinawa
 --Kabilun kasar Sin
[ Bunkasuwa ]
 --Tattalin arziki
 --Bunkasuwar Sin
[ Yawon shakatawa ]
 --Yawo a kasar Sin
 --Wurare masu yawo
[ Ilmi, Lafiya ]
 --Fagen bincike
 --Kiwon lafiya
[ Wasanni ]
 --Labaran wasannin
 --Me ka sani
(GMT+08:00) 2008-01-23 09:33:27    
Tarzomar Kenya ta kawo babbar illa ga tattalin arzikin yankin Gabashin Afirka

cri

Rikicin siyasa na kasar Kenya da aka dade ba a warware shi ba ba kawai ya kawo wa wannan kasa mummunar illa a harkokin tattalin arziki ba, har ma ya haddasa jerin matsaloli a yankin Gabashin Afirka, kasashe na wannan yanki sun sami babbar illa a harkokin bunkasuwar tattalin arziki.

In an kwatanta da sauran kasashen Gabashin Afirka, muna iya ganin cewa, an dade ana tabbatar da kwanciyar hankali a harkokin siyasa a Kenya, kuma Kenya tana raya tattalin arziki ta hanyoyi daban daban. Kyakkyawan wurin da take ciki ya sanya Kenya ta zama cibiyar yankin Gabashin Afirka a fannonin tattalin arziki da sufuri sannu a hankali, haka kuma ita ce muhimmiyar kasa da kasashe masu makwabtaka da ita suke yi ciniki da ita.

Tun bayan da kwamitin kula da harkokin zabe na Kenya ya sanar da cewa, Mr. Kibaki ya sami nasarar babban zabe, ya sake zama shugaan Kenya a karshen shekarar bara, jam'iyyar 'yan hamayya wato jam'iyyar ODM ta ki amincewa da sakamakon zaben, ta kuma yi ikirari cewa, an yi mummunan magudi a babban zaben. Daga baya kuma, babbar tarzoma da aka samu a wurare daban daban na Kenya ta zama sanadiyyar mutuwar daruruwan mutane, yayin da mutane kimanin dubu 250 suka rasa wuraren kwana, ta kuma yi wa Kenya asarar dalar Amurka misalin biliyan 1.

Kazalika kuma, tarzomar da aka samu a Kenya ta kawo illa ga harkokin ciniki a tsakaninta da kasashe masu makwabtaka da ita. Kenya kasa ce ta biyu da ta zuba wa kasar Tanzania jari. Bayan aukuwar tarzomar, yawan kudaden da kasashen 2 suka samu daga wajen yin ciniki a tsakaninsu ya ragu. A watan jiya na wannan shekara, yawan kudaden haraji da suka samu a bakin iyakarsu ya sami raguwa sosai. Saboda an datse hanyoyi, shi ya sa aka raunana ayyukan shige da fice a tsakanin Kenya da kasar Uganda.

Kenya cibiya ce ta sufuri a gabashin Afirka. A ko wace rana, a kan yi jigilar dimbin kayayyaki zuwa sauran kasashen gabashin Afirka daga tashar jiragen ruwa ta Mombasa. Wannan tashar jiragen ruwa ita ce kusan karfin rayuwar kasashen gabashin Afirka wajen raya tattalin arziki. Bankin Kasa da Kasa ya kimanta cewa, Uganda da Ruwanda suna dogara da hanyoyin da ke tsakaninsu da Mombasa domin samun jimlar GNP na yawan kashi 25 cikin kashi dari, irin wannan adadin ya kai kashi 33 cikin kashi dari ga kasar Burundi.

Tarzomar ta datse hanyoyin sufuri a tsakanin Mambasa da wadannan kasashen gabashin Afirka marasa mafitan teku, shi ya sa wadannan kasashe suke fama da karancin kayayyaki, haka kuma, suna fuskantar matukar hauhawar farashin kaya.

Abu mafi tsanani da wadannan kasashe ke fuskanta shi ne datse hanyoyin samar da man fetur ya sanya su cikin mawuyancin hali na karancin man fetur. A cikin kwanaki da dama kawai, an sayar da kusan dukkan gas a birnin Kampala, hedkwatar Uganda. A wasu tashoshin gas da suke da gas kadan, farashin gas ya taba kai dalar Amurka 5 a ko wace litre. Sa'an nan kuma, saboda karancin man fetur, Uganda ta dakatar da sufurin jiragen sama a gida na wucin gadi.


1 2