Sin ciki da waje (chinaabc)Rediyon kasar SinSashen Hausa
China Radio International
Labarun gida
Labarun duniya
Labarun Siyasa
Labarun Tattalin Arziki
Labarun Al'adu
Labarun Wasanni
Sauran Labaru
Saurari labarai da dumi-duminsu da sauran shirye-shirye
more>>
[ Al'adu ]
 --Al'adun Sinawa
 --Kabilun kasar Sin
[ Bunkasuwa ]
 --Tattalin arziki
 --Bunkasuwar Sin
[ Yawon shakatawa ]
 --Yawo a kasar Sin
 --Wurare masu yawo
[ Ilmi, Lafiya ]
 --Fagen bincike
 --Kiwon lafiya
[ Wasanni ]
 --Labaran wasannin
 --Me ka sani
(GMT+08:00) 2008-01-22 21:46:21    
Wahalolin da aka sha a Zirin Gaza tare da rikicin da ke tsakanin Palesdinu da Isra'ila wajen shimfida zaman lafiya

cri

Mawuyacin halin da ake ciki a Zirin Gaza ya riga ya jawo damuwar hankula daga gamayyar kasa da kasa. A ranar 18 ga wannan wata da kasar Isra'ila ta soma yin kangiya a zirin Gaza daga dukkan fannoni, babban sakataren Majalisar Dinkin duniya Mr Ban Ki-Moon ya bayar da sanarwa, inda ya mai da hankali sosai ga aikin da kudurin da Isra'ila ta tsaida. Sanarwar ta kira dakarun Palesdinu cikin gaggawa don dakatar da farmakin da suke yi wa Isra'ila ta hanyar yin amfani da bindigogi da harsashen roket, a sa'I daya kuma ya kirayi sojojin tsaron kasa na Isra'ila da su yi hakuri. A ranar 21 ga wannan wata, kungiyar tarayyar kasashen Larabawa ta bayar da sanarwa, inda ta sa kaimi ga kwamitin sulhu na Majalisarsa da ya kira taro don hana aikin da Isra'ila take yi a Zirin Gaza a daidai lokaci, da kuma sa kaimi ga Isra'ila da ta bude kofar tashoshin wucewar iyakar kasa don kiyaye hakkin dan adam na mutanen wurin. A wannan rana kuma, kungiyar tarayyar kasashen Turai ita ma ta bayar da sanarwa, inda a lokacin da ta kai suka kan farmakin da dakarun Palesdinu ta yi ta hanyar yin afmani da harsashen roka da kuma kiran bangarorin biyu da su dakatar da bude wutar yaki, ta kuma bayyana cewa, kangiyar da Isra'ila ta yi zai kara tsananin rikicin jinkai a Zirin Gaza.

Game da halin da ake ciki, firayim ministan kasar Isra'ila Ehud Olmert ya bayyana a wannan rana cewa, ba za a yarda da faruwar rikicin jinkai ba. Amma ya cigaba da jaddada cewa, bisa halin da ake ciki na rashin tabbatar da samun kwanciyar hankali ga zaman rayuwar mazaunan kudancin Isra'ila, to mutanen Zirin Gaza su ma ba za su iya yin zaman rayuwa cikin nishadi ba.

Amma, ana shakka sosai a kan ko za a iya hana farmakin da dakarun Palesdinu suke yi da harsashen roka ta hanyar kafa kangiya da kai farmakin soja.(Halima)


1 2