Sin ciki da waje (chinaabc)Rediyon kasar SinSashen Hausa
China Radio International
Labarun gida
Labarun duniya
Labarun Siyasa
Labarun Tattalin Arziki
Labarun Al'adu
Labarun Wasanni
Sauran Labaru
Saurari labarai da dumi-duminsu da sauran shirye-shirye
more>>
[ Al'adu ]
 --Al'adun Sinawa
 --Kabilun kasar Sin
[ Bunkasuwa ]
 --Tattalin arziki
 --Bunkasuwar Sin
[ Yawon shakatawa ]
 --Yawo a kasar Sin
 --Wurare masu yawo
[ Ilmi, Lafiya ]
 --Fagen bincike
 --Kiwon lafiya
[ Wasanni ]
 --Labaran wasannin
 --Me ka sani
(GMT+08:00) 2008-01-22 21:46:21    
Wahalolin da aka sha a Zirin Gaza tare da rikicin da ke tsakanin Palesdinu da Isra'ila wajen shimfida zaman lafiya

cri

Kwanakin nan, an sake haifar da hali mai zafi a shiyyar Palesdinu da Isra'ila, lokacin aikin sa kangiya da Isra'ila take yi wa dakarun Palesdinu a dukan fannoni don tilasta musu wajen sa aya ga harba roka a kudancin kasar Isra'ila ya riga ya kai kwanaki hudu, mazaunan Zirin Gaza wadanda suke zama ba dadi suna kara shan wahaloli a yau da kullum.

Da ya ke akwai karancin makamashi bisa sakamakon kangiyar da aka yi, a ranar 20 ga wannan wata, ma'aikatar samar da karfin lantarki ta Zirin Gaza ta riga ta daina aiki da dukkan na'urorin samar da karfin lantarki, saboda haka birnin Gaza ya shiga duhu , sa'anan kuma tashoshin kara mai su ma sun rufe kofofinsu, haka kuma shagunan sayar da Burodi su ma sun rufe kofofinsu, asibitoci su ma suna karancin makamashin da ake yin amfani da su don samar da karfin lantarki. Dayake rashin karfin lantarki, shi ya sa ba a iya yin amfani da firji, sa'anan kuma farashin abincin da suke hada da nama da madara shi ma ya kara hauhawa, daga cikinsu, farashin nama ya karu da ninki daya a cikin yan kwanaki goma da suka wuce.

Yanzu, abincin da yawancin mutanen da suke cikin mutane miliyan 1.5 na Zirin Gaza suke bukata ya dogara da taimakon agajin da aka samar musu. Amma, aikin hukumar samar da taimakon agaji ta Majalisar dinkin duniya shi ma ya shiga mawuyacin hali bisa sakamakon kangiyar da aka yi. A ranar 21 ga wannan wata, kakakin hukumar kula da ayyukan ba da taimakon agaji ta Majalisar Dinkin duniya Mr Chiris Gunness ya bayyana cewa, dayake Isra'ila ta yi wa Zirin Gaza kangiya, shi ya sa hukumarsa ta riga ta kusanci rashin samun makamashin yin jigilar abinci da lidar da ake yin amfani da su don rarraba abinci, in ana ci gaba da kasancewa cikin halin nan, to aikin ba da taimakon agaji da hukumar take yi a Zirin, mai yiyuwa ne zai sa aya a ranar 24 ko 25 ga watan da muke ciki. Bisa labarin da hukumar tsara shirin abinci ta duniya ta tono, an bayyana cewa, kayayyakin da hukumar ta yi don ba da taimakon agaji za su kare a karshen makon da muke ciki.


1 2