Sin ciki da waje (chinaabc)Rediyon kasar SinSashen Hausa
China Radio International
Labarun gida
Labarun duniya
Labarun Siyasa
Labarun Tattalin Arziki
Labarun Al'adu
Labarun Wasanni
Sauran Labaru
Saurari labarai da dumi-duminsu da sauran shirye-shirye
more>>
[ Al'adu ]
 --Al'adun Sinawa
 --Kabilun kasar Sin
[ Bunkasuwa ]
 --Tattalin arziki
 --Bunkasuwar Sin
[ Yawon shakatawa ]
 --Yawo a kasar Sin
 --Wurare masu yawo
[ Ilmi, Lafiya ]
 --Fagen bincike
 --Kiwon lafiya
[ Wasanni ]
 --Labaran wasannin
 --Me ka sani
(GMT+08:00) 2008-01-22 18:13:19    
Asibitin Chang Geng na Xiamen da kamfanin roba na Taiwan ya kafa

cri

Dakta Huang Dehai na sashen nazarin batun Taiwan na jami'ar Tsinghua na kasar Sin, yana ganin cewa, muhimman dalilai guda biyu kai tsaye da ke sanya asibitocin Taiwan su shiga kasuwar aikin likita ta babban yankin kasar Sin su ne, da farko, 'yan kasuwa na Taiwan da ke zuba jari a babban yankin kasar Sin suna da yawa, kuma mutanen Taiwan da ke yin yawon shakatawa suna ta karuwa. A waje daya kuma, kasuwar likita ta Taiwan na jike jagab, amma a babban yankin kasar Sin, kasuwar na da boyayen karfi sosai. Wannan dalili ne mafi zurfi.

Ban da asibitin WantWant, da kuma asibitin Chang Geng na birnin Xiamen, akwai hukumomin likita da yawa na Taiwan suna shirya kafa asibitoci a babban yankin kasar Sin. Dakta Huang Dehai ya bayyana cewa, bayan sana'ar kira, yanzu ana kara yin cudanya a tsakanin hukumomin aikin likita na gabobin 2 na mashigin teku na taiwan.

"Bisa sana'ar kira, ana ja da baya wajen bude kofa a fannin sana'ar ba da hidima ta aikin likita, amma ba za a canja manufar ci gaba da bude kofa wajen aikin likita ba, ana iya amincewa da cewa, aikin likita na babban yankin kasar Sin zai zama muhimmin aiki daban da hukumomin aikin likita na Taiwan ke gudanarwa.


1 2