Sin ciki da waje (chinaabc)Rediyon kasar SinSashen Hausa
China Radio International
Labarun gida
Labarun duniya
Labarun Siyasa
Labarun Tattalin Arziki
Labarun Al'adu
Labarun Wasanni
Sauran Labaru
Saurari labarai da dumi-duminsu da sauran shirye-shirye
more>>
[ Al'adu ]
 --Al'adun Sinawa
 --Kabilun kasar Sin
[ Bunkasuwa ]
 --Tattalin arziki
 --Bunkasuwar Sin
[ Yawon shakatawa ]
 --Yawo a kasar Sin
 --Wurare masu yawo
[ Ilmi, Lafiya ]
 --Fagen bincike
 --Kiwon lafiya
[ Wasanni ]
 --Labaran wasannin
 --Me ka sani
(GMT+08:00) 2008-01-22 18:13:19    
Asibitin Chang Geng na Xiamen da kamfanin roba na Taiwan ya kafa

cri

Ta shirye-shiryen da aka yi har shekaru biyu, cibiyar aikin likita ta farko da asibitin Chang Geng na Taiwan ya kafa a babban yankin kasar Sin, za ta soma aiki ba da dadewa ba a birnin Xiamen na jihar Fujian da ke kudu maso gabashin kasar Sin. Tun bayan da gwamnatin tsakiyar kasar Sin ta fitar da manufofin da abin ya shafa a shekarar 2000, don amincewa da kamfanonin Taiwan da su kafa asibitoci a babban yankin kasar Sin ta hanyar zuba jari tare, wasu kamfanoni da hukumomin kula da aikin likita na Taiwan masu hangen nesa, sun soma kafa asibitoci daya bayan daya a babban yankin kasar Sin. A cikin shirinmu na yau, za mu yi muku bayani kan halin da ake ciki dangane da yadda ake gudanar hukumomin aikin likita da aka zuba jari tare a babban yankin kasar Sin.

Asibitin Chang Geng na Xiamen da kamfanin roba na Taiwan ya kafa, yana yankin zuba jari na 'yan kasuwar Taiwan, fadin muraba'insa ya kai ekoki 70, kuma ya hada da sassa guda uku, wato yankin asibiti, da makarantar aikin likita, da kuma kauyen koshin lafiya. Jimlar kudin da aka zuba kan asibitin ya kai kusan kudin Sin RMB yuan biliyan 1.2. Shugaban asibitin Chang Geng na Xiamen Mr. Zheng Minghui ya bayyana cewa, ana kasancewa da wani teku kawai a tsakanin birnin Xiamen da Taiwan, saboda haka, 'yan kasuwa na Taiwan da ke zuba jari a birnin Xiamen suna da yawa, wani muhimmin dalilin da ya sa aka zabi Xiamen, don kafa asibitin Chang Geng shi ne, ba da hidima ga 'yan kasuwa na Taiwan da ke shiyyar.

'Yan kasuwa na Taiwan za su saba da asibitin Chang Geng. Saboda asibitin Chang Geng na birnin Xiamen ya yi daidai kamar na Taiwan. Bayan haka kuma, asibitinmu na iya samun halin ciwo na wadannan 'yan kasuwa da ke Taiwan, ta hanyar yin amfani da tsarin na'urar electronic."

A matsayinsa na asibiti na farko da aka kafa da jarin Taiwan a babban yankin kasar Sin, asibitin WantWant na birnin Changsha na lardin Hunan ya riga ya soma aiki har shekaru 2. Shugaban asibitin Mr. Li Yongguo ya gayawa wakilinmu cewa, sun zabi jihar Hunan don kafa asibitin ne, bayan da suka yi nazari sosai kan yiwuwar gudawarwa a kasuwa:

"Akwai mutane sama da miliyan 67 a jihar Hunan, wato ya ninka sau uku bisa na Taiwan. Amma, manyan asibitoci na jihar ba su da yawa. Bayan haka kuma, aikin likita na jihohin da ke makwabtaka da jihar Hunan, ciki har da jihohin Guangxi, da Jiangxi, da kuma Guizhou, bai samu ci gaba sosai ba."


1 2