Bayan haka, masallacin ya hada sigar timba ta gargajiya ta kasar Sin da fasahohin sassakar itace na musulunci tare, wanda ya nuna mana sakamako mai kyau daga aka samu daga yin cudanyar al'adu a tsakanin kabilu daban daban da ke jihar.
Masu karatu, mun dai yi muku takaitaccen bayani a kan musulmi a kasar Sin da kuma masallacin Tongxin na kasar. Idan kuna sha'awar bunkasuwar musulunci a kasar Sin, muna muku marhabin da sauraron shirinmu na musulunci a kasar Sin, inda Bilkisu ke kawo muku labarai iri iri masu kayatarwa da ke shafar zaman rayuwar musulmi a kasar Sin a fannoni daban daban, kada kuma ku manta wannan shiri na zuwa muku ne a kowace ranar Alhamis daga nan sashen Hausa na rediyon kasar Sin, sai mu hadu a filin a kowace ranar Alhamis.(Lubabatu) 1 2
|