Sin ciki da waje (chinaabc)Rediyon kasar SinSashen Hausa
China Radio International
Labarun gida
Labarun duniya
Labarun Siyasa
Labarun Tattalin Arziki
Labarun Al'adu
Labarun Wasanni
Sauran Labaru
Saurari labarai da dumi-duminsu da sauran shirye-shirye
more>>
[ Al'adu ]
 --Al'adun Sinawa
 --Kabilun kasar Sin
[ Bunkasuwa ]
 --Tattalin arziki
 --Bunkasuwar Sin
[ Yawon shakatawa ]
 --Yawo a kasar Sin
 --Wurare masu yawo
[ Ilmi, Lafiya ]
 --Fagen bincike
 --Kiwon lafiya
[ Wasanni ]
 --Labaran wasannin
 --Me ka sani
(GMT+08:00) 2008-01-18 18:00:16    
Musulmi a kasar Sin

cri

Tambayar da za mu amsa a wannan mako ta fito ne daga hannun Shehu Abdullahi Dandume, wanda bai bayyana mana wurin da ya fito ba. A cikin wasikar da malamin ya turo mana, ya tambaye mu, kamar mutane nawa ke musulmai a kasar Sin? Ko suna da sunaye kamar namu da ya shafi musulunci? A wace jiha wadannan musulmai suka fi yawa a kasar Sin? To, a hakika, mu sha samun tambayoyin masu sauraro dangane da musulmi a kasar Sin, misali, ko akwai musulmi a kasar Sin? yaya zaman rayuwarsu a fannoni daban daban? A hakika a shirye-shiryenmu na da, mun taba muku bayani, to, amma duk da haka, sabo da watakila akwai masu sauraron da suka wuce shirye-shiryen, amma ga shi suna sha'awar batun, to, a cikin shirinmu na yau, bari mu kara muku bayani a kan musulmi na kasar Sin. Sa'an nan, domin amsa tambayar malam Alhasan Juma, mazaunin garin Dukku, jihar Gombe, tarayyar Nijeriya, za mu dan bayyana muku tarihin masallacin Tongxin na jihar Ningxia.

Kasar Sin kasa ce da ke da mabiyan addinai iri daban daban, ciki har da Buddhism da Daoism da Musulunci da Katolika da kuma kirista. Daga cikinsu, musulunci ya yadu har zuwa kasar Sin ne a karni na 7, daga baya, a karni na 13, musulunci ya riga ya bunkasa har ya zama wani addinin da ya sami dimbin mabiyansa a kasar Sin. A yanzu haka dai, akwai mutane fiye da miliyan 20 na bin musulunci a kasar Sin, kuma yawan masallatai da ke a kasar ya kai fiye da dubu 30, a yayin da limamai suka wuce dubu 40. Bayan haka, yawancin musulmai na kasar Sin suna da sunaye na Sinanci ko kuma na yaren kabilarsu, a yayin da suke kuma da wani suna na daban na musulunci. A nan kasar Sin, musulmai suna babbar sallah da kuma karamar sallah kamar yadda musulmai a sauran kasashe ke yi. Sa'an nan, a game da jihar da musulmai suka fi yawa a kasar Sin, yawancin musulmi na kasar Sin suna zama ne a jihar Xinjiang da jihar Ningxia da ke arewa maso yammacin kasar, sa'an nan, a jihohin Gansu da Qinghai da Yunnan da dai sauran jihohi da biranen kasar, akwai kuma musulmai da ke zaune a can.

To, domin amsa tambayar malam Alhasan Juma, mazaunin garin Dukku, jihar Gombe, tarayyar Nijeriya, yanzu bari mu kai ziyara a wani shahararren masallacin da ke jihar Ningxia ta kasar Sin. Jihar Ningxia jiha ce mai zaman kanta ta 'yan kabilar Hui, kuma kabilar Hui na daya daga cikin kabilu goma na kasar Sin wadanda ke bin musulunci. Sakamakon dimbin 'yan kabilar Hui musulmai da ke zaune a jihar Ningxia, Ningxia ta kuma zama jiha ta musulmi a kasar Sin, har ma gaba daya akwai masallatai da suka wuce 3,000 a jihar, kuma masallacin Tongxin na daya daga cikinsu. Masallacin yana kan wani tudun da ke arewa maso yammacin tsohuwar gundumar Tongxin, kuma an kafa shi ne a daular Ming wato tsakanin shekara ta 1573 zuwa 1619, sabo da haka masallacin ya zama daya daga cikin masallatai masu girma da kuma dogon tarihi a jihar Ningxia. Sifar masallacin Tongxin tana shan bamban da sauran masallatai na kasar Sin, ya yi kama da wata fada. An gina wannan masallaci a kan wani tudun da tsayinsa ya kai mita 10 kuma fadinsa ya kai murabba'in mita 3500. Gine-gine mafi muhimmanci na masallacin su ne babban dakin yin salla da kuma Mi'dhanah, inda musulmai kusan 1000 suke iya yin salla tare.

1 2