Ba da ra'ayin wai yin barazana daga kasar Iran" da kuma kebantar da ita ya zama wani muhimmin makasudi daban da Mr. Bush ya dauka wajen ziyarar da ya yi a wannan gami a Gabas ta tsakiya. A yayin da Bush yake ganawa da shugabannin kasashen Gabas ta tsakiya, ba sau daya ba ba sau 2 baya ya kai suka kan kasar Iran, ya bayyana cewa, shirin tace sinadarin Uranium da kasar Iran ke yi ya jawo banazana ga shiyyar kuma ga duk duniya baki daya, kuma ya zargi Iran wai ta tsoma baki cikin harkokin gida na kasar Lebanon.
Amma kokarin da Bush ya yi a wannan fanni bai samu martani sosai daga wajen kasashen Larabawa masu abuta da shi ba, sai dai sun saurari ra'ayinsa da ladabi kawai, amma bai iya canza ra'ayin da suka dauka kan kasar Iran ba.
Wani muhimmin abun da ya kamata a sa lura a kai a gun ziyarar da Mr. Bush ya yi a Gabas ta tsakiya shi ne matsalar man fetur. Yayin da Bush yake ganawa da sarkin kasar Sa'udiya Abdullah bin abdul Aziz ya bayyana cewa, yana fatan kasashe mambobin kungiyar OPEC za su kada kuri'un nuna goyon bayansu ga kara fitar da man fetur da yawa, amma bangaren Sa'udiya ya bayyana cewa, karuwar yawan man fetur da za a fitar ya danganta ne bisa ga halin da ake ciki a kasuwanni, amma bai mayar da martani daidai bisa bukatar da Amurka ke yi ba. (Umaru) 1 2
|