Sin ciki da waje (chinaabc)Rediyon kasar SinSashen Hausa
China Radio International
Labarun gida
Labarun duniya
Labarun Siyasa
Labarun Tattalin Arziki
Labarun Al'adu
Labarun Wasanni
Sauran Labaru
Saurari labarai da dumi-duminsu da sauran shirye-shirye
more>>
[ Al'adu ]
 --Al'adun Sinawa
 --Kabilun kasar Sin
[ Bunkasuwa ]
 --Tattalin arziki
 --Bunkasuwar Sin
[ Yawon shakatawa ]
 --Yawo a kasar Sin
 --Wurare masu yawo
[ Ilmi, Lafiya ]
 --Fagen bincike
 --Kiwon lafiya
[ Wasanni ]
 --Labaran wasannin
 --Me ka sani
(GMT+08:00) 2008-01-17 14:29:40    
Ziyarar da Mr, Bush ya yi a Gabas ta tsakiya ta sami sakamako kadan

cri

A ran 16 ga wata, shugaba Bush na Amurka ya tashi daga kasar Masar wato ya sa aya ga ziyarar da ya shafe kwanaki 8 yana yi a kasashe 6 na Gabas ta tsakiya. Kada a musunta cewa, ziyarar da Mr. Bush ya yi a Gabas ta tsakiya ta kawo karfin zuciya ga shawarwarin da ake yi tsakanin Palesdinu da Isra'ila domin shimfida zaman lafiya, amma idan ana son tabbatar da wannan kyakkyawan fata, har ila yau ya kasance da doguwar hanya da za a bi. Amma a fannin kaddamar da manufarsa kan kasar Iran da shawo kan kungiyar Opec da ta daga farashin gurbataccen man fetur, Mr. Bush bai samu cikakken goyon baya daga wajen kawayensa Larabawa ba.

Sa kaimi ga yin shawarwarin shimfida zaman lafiya tsakanin Palesdinu da Isra'ila ya zama makasudi na farko ne ga Mr. Bush wajen yin wannan ziyara. A lokacin da Bush yake saduwa da shugabannin Palesdinu da Isra'ila ya bayyana cewa, ya ji dadi ga bangarorin 2 wato Palesdinu da isra'ila wadanda suka daddale yarjejeniyar shimfida zaman lafiya cikin shekara daya kawai, kuma shugabannin Palesdinu da Isra'ila sun ba da taimako ga Mr. Bush daga dukkan fannoni. Amma bayan saduwar da aka yi tsakaninsu, matsayin da wadannan bangarori 2 suka dauka bai sauya sosai, dukkansu 2 ba su tabbatar da cewa, za su ciyar da shawarwarin shimfida zaman lafiya gaba daidai bisa bukatar da Amurka ta yi musu ba.

Manazarta sun bayyana cewa, bayan da Mr. Bush ya tashi daga Gabas ta tsakiya don komawa gidansa, irin kokarin da ya yi bai tabbati ba. A hakika kuwa, a ranar da ya tashi daga Gabas ta tsakiya kuma 'yan ra'ayin mazan jiya na kasar Isra'ila wato kungiyar "Isra'ila ita ce kasa mahaifarmu" ta yi shelar janye jikinta daga kawancen mulkin kasar sabo da rashin yarda da manufar da Mr. Ehud Olmert ya dauka na sayar da yankunan kasa domin samun zaman lafiya, wannan ya zama babban bugu ne ga gwamnatin Olmer wadda take bukatar samun goyon baya daga fannoni daban-daban domin daddale yarjejeniya tsakaninsa da Palesdinu. Don su kasashen Larabawa kuwa, ko da yake a birnin Kudus Mr. Bush ya yi musu kira don su yi mu'amala da Isra'ila, amma har ila yau babu wata kasar Larabawa da ta mayar da martani ga kiran da Mr. Bush ya yi, a akasin haka kuwa, kafofin watsa labaru na wannan wuri sun yi shakka ga fatan da Mr. Bush ya yi na neman zama madugun shimfida zaman lafiya a Gabas ta tsakiya.

1 2