Kasashen Sin da Indiya kasashe ne masu tasowa da suka fi girma a duniya. A cikin 'yan shekarun nan da suka wuce, huldar cinikayya da ke tsakanin kasashen biyu ma ta samu cigaba cikin sauri. Shugabannin kasashen biyu dukkansu sun ce za a kara raya huldar tattalin arziki da cinikayya a tsakanin kasashen biyu. Mr. Singh ya ce, "Muna ganin cewa, ya kamata mu raya huldar abokantaka irin ta hadin gwiwa bisa manyan tsare-tsare a tsakaninmu bisa bunkasuwar huldar tattalin arziki da cinikayya irin ta moriyar juna a fannoni daban-dabam. Mun tsai da kuduri tare cewa, ya kamata jimlar kudaden cinikayya da za a samu a shekarar 2010 ta kai dalar Amurka biliyan 60 maimaikon dalar Amurka biliyan 40 ta yanzu."
Bugu da kari kuma, Mr. Wen Jiabao da Mr. Singh sun rattaba hannu tare kan wata takarda mai suna 'buri daya da kasashen Sin da Indiya suke nema cimmawa a karni na 21', inda suka bayyana cewa, za su raya huldar abokantaka irin ta hadin gwiwa domin tabbatar da zaman lafiya da samun bunkasuwa tare a tsakanin kasashen biyu. Game da wannan takarda, Mr. Wen Jiabao ya ce, "Mun yarda da kara yin hadin gwiwa kan batutuwan kasa da kasa da na shiyya-shiyya domin sa kaimi wajen raya wata zaman al'umma mai jituwa da ke da zaman lafiya mai dorewa da bunkasuwa. Wannan takarda tana bayyana ra'ayi daya da muka samu kan muhimman batutuwan kasa da kasa da na shiyya-shiyya. Sakamakon haka, tabbas ne wannan takarda za ta zama wata muhimmiyar takarda daban da ke ba da jagoranci ga kokarin raya huldar da ke tsakanin Sin da Indiya." 1 2
|