Sin ciki da waje (chinaabc)Rediyon kasar SinSashen Hausa
China Radio International
Labarun gida
Labarun duniya
Labarun Siyasa
Labarun Tattalin Arziki
Labarun Al'adu
Labarun Wasanni
Sauran Labaru
Saurari labarai da dumi-duminsu da sauran shirye-shirye
more>>
[ Al'adu ]
 --Al'adun Sinawa
 --Kabilun kasar Sin
[ Bunkasuwa ]
 --Tattalin arziki
 --Bunkasuwar Sin
[ Yawon shakatawa ]
 --Yawo a kasar Sin
 --Wurare masu yawo
[ Ilmi, Lafiya ]
 --Fagen bincike
 --Kiwon lafiya
[ Wasanni ]
 --Labaran wasannin
 --Me ka sani
(GMT+08:00) 2008-01-15 18:49:21    
Kasashen Sin da Indiya za su kara raya huldar abokantaka irin ta hadin guiwa bisa manyan tsare-tsare a tsakaninsu

cri

A ran 14 ga wata da yamma, firayin ministan kasar Sin Wen Jiabao ya yi shawarwari da takwaransa na kasar Indiya Manmohan Singh wanda ke yin ziyara a nan kasar Sin, inda bangarorin biyu suka sami ra'ayi daya kan yadda za su kara raya huldar abokantaka irin ta hadin gwiwa bisa manyan tsare-tsare a cikin sabon halin da ake ciki yanzu. Bangarorin biyu duka sun yarda da cewa, za su sa kaimi ga kokarin raya wata zaman al'umma mai jituwa da ke tabbatar da zaman lafiya da bunkasuwa mai dorewa a duk fadin duniya ta hanyar raya huldar abokantaka irin ta hadin guiwa bisa manyan tsare-tsare a tsakanin kasashen biyu da ke shafar zaman lafiya da bunkasuwa.

Wannan ne karo na farko da Mr. Singh ya yi ziyara a kasashen waje a shekara ta 2008. Sabo da haka, masana sun bayyana cewa, wannan ya bayyana cewa, Mr. Singh yana mai da hankali sosai kan huldar da ke tsakanin Indiya da kasar Sin. Lokacin da yake shawarwari tare da Mr. Wen Jiabao, Mr. Singh ya kuma tabbatar da cewa, "Muna mai da hankulanmu sosai wajen raya huldar hadin guiwa irin ta moriyar juna a tsakaninmu da kasar Sin. Ziyarce-ziyarcen da shugabannin kasashen biyu suka kai wa juna a kullum suna raya huldar da ke tsakaninmu cikin sauri. Irin wadannan ziyarce-ziyarce da musanye-musanye sun bayyana wa duniya cewa, muna da niyyar kara fahimtar juna da amincewa da juna a tsakaninsu."

Mr. Singh ya kara da cewa, manufar raya huldar da ke tsakanin Indiya da kasar Sin tana kan gaba daga cikin manufofin diplomasiyya da kasar Indiya take aiwatarwa.

Mr. Wen Jiabao da Mr. Singh sun yi kusan sa'o'i biyu suna shawarwari. Bayan shawarwarin, Mr. Wen Jiabao ya gaya wa manema labaru cewa, "Muna ganin cewa, kasashen Sin da Indiya abokai ne na yin hadin gwiwa, ba abokai ne na yin takara ba. Ya kamata kasashen Sin da Indiya su girmama juna da fahimtar juna da amince da juna da yin hadin gwiwa domin moriyar juna, amma ba wani ya wuce wani daban ba. Kara saurin karfafa takaitaccen karfi na kasashen biyu zai samar da dama ga kokarin zurfafa huldar da ke tsakanin bangarorin biyu. Idan [asashen Sin da Indiya suka [ara yin hadin guiwa a tsakaninsu, hakan zai amfana wa zaman lafiya da cigaban Asiya har na duk duniya."

1 2