Sin ciki da waje (chinaabc)Rediyon kasar SinSashen Hausa
China Radio International
Labarun gida
Labarun duniya
Labarun Siyasa
Labarun Tattalin Arziki
Labarun Al'adu
Labarun Wasanni
Sauran Labaru
Saurari labarai da dumi-duminsu da sauran shirye-shirye
more>>
[ Al'adu ]
 --Al'adun Sinawa
 --Kabilun kasar Sin
[ Bunkasuwa ]
 --Tattalin arziki
 --Bunkasuwar Sin
[ Yawon shakatawa ]
 --Yawo a kasar Sin
 --Wurare masu yawo
[ Ilmi, Lafiya ]
 --Fagen bincike
 --Kiwon lafiya
[ Wasanni ]
 --Labaran wasannin
 --Me ka sani
(GMT+08:00) 2008-01-15 16:28:50    
Gidan ibada na Wanshousi, wato dakin nune-nunen kayayyakin fasaha na Beijing

cri

Yanzu an yi wa gidan ibada na Wanshousi kwaskwarima zuwa dakin nune-nunen kayayyakin fasaha na Beijing, inda abubuwan fasaha na zamanin daular Ming da Qing suka sami rinjaye. Ana ajiye abubuwan fasaha iri daban daban fiye da dubu 70 a wannan gidan ibada, a ciki har da rubuce-rubucen da aka yi da hannu da zane-zane da abubuwan dinki da tangaran da kayayyakin daki na katako da dai sauransu. Wurin da aka ware domin nuna tangaran ya fi nuna sigar musamman. Madam Sun ta gaya mana cewa,'Tangaran da ake nunawa a gidan ibadanmu sun fi nuna sigar musamman ta fasahar kera tangaran irin na zamanin daular Ming da Qing na kasar Sin. Ga wannan faranti da aka yi zane-zanen 'ya'yan zaki wato Peach guda 8 a kansa, laununakan wadannan Peach guda 8 na shan bamban da juna. Kyan ganin farantin nan ya yi daidai da zane-zanen gargajiya na kasar Sin. An yi zane-zane aba tsayawa a duk cibiyar farantin da kuma wajensa. An kera wannan faranti ne domin nuna fatan alheri, wato samun alheri da kuma tsawon rai.'

Kazalika kuma, bukukuwan nune-nunen abubuwan fasaha na addinin Buddha da wadanda aka yi da hannu na zamanin daular Ming da Qing da aka shirya a gidan ibada na Wanshousi su ma sun jawo hankulan mutane.

Dakin nune-nunen kayayyakin fasaha na Beijing ya nuna ainihin fasahar gargajiya ta kasar Sin daga bangarori daban daban. Ya yi suna ne a gida da kuma a ketare a matsayin lu'ulu'un da ke nuna ainihin fasahar al'ummar kasar Sin. In kuna sha'awarsa, to, ya fi kyau ku kawo masa ziyara da kanku.


1 2