Sin ciki da waje (chinaabc)Rediyon kasar SinSashen Hausa
China Radio International
Labarun gida
Labarun duniya
Labarun Siyasa
Labarun Tattalin Arziki
Labarun Al'adu
Labarun Wasanni
Sauran Labaru
Saurari labarai da dumi-duminsu da sauran shirye-shirye
more>>
[ Al'adu ]
 --Al'adun Sinawa
 --Kabilun kasar Sin
[ Bunkasuwa ]
 --Tattalin arziki
 --Bunkasuwar Sin
[ Yawon shakatawa ]
 --Yawo a kasar Sin
 --Wurare masu yawo
[ Ilmi, Lafiya ]
 --Fagen bincike
 --Kiwon lafiya
[ Wasanni ]
 --Labaran wasannin
 --Me ka sani
(GMT+08:00) 2008-01-15 16:28:50    
Gidan ibada na Wanshousi, wato dakin nune-nunen kayayyakin fasaha na Beijing

cri

A arewacin Beijing, akwai wani gidan ibada mai tsawon shekaru misalin 430, sunansa shi ne Wanshousi. A da, wannan gidan ibada ya taba kasancewa a matsayin wurin da masarautan kasar Sin na zamanin daular Ming da Qing suka shirya bukukuwa da kuma yada zango, shi ya sa a kan kira shi 'karamar fadar sarakuna ta kasar Sin wato karamin Forbidden City'. Ana ajiye zane-zane da rubuce-rubuce da aka yi da hannu da kayayyakin dinki da tangaran da sauran abubuwan fasaha fiye da dubu 70 a cikin wannan gidan ibada. Dimbin masu yawon shakatawa na gida da na waje suna ta kawo masa ziyara.

Kong Xiangli, wani kwararre mai ilmin gidan ibada na Wanshousi, ya yi shekaru kusan 20 yana nazarin wannan gida ibada. Game da asalin wannan gidan ibada, ya yi karin bayani cewa,'An gina gidan ibada na Wanshousi a shekarar 1577. Kafuwarta tana da nasaba da masarauta sosai. A zamanin daular Ming, a lokacin da sarkin Wanli yake kan kujerar mulki, matarta ta gaskata da addinin Buddha kwarai. A lokacin, saboda wani wurin da gwamnatin ta ajiye littattafan addinin Buddha ya lalata, shi ya sa aka yi shirin yi masa kwaskwarima. Mamar sarkin Wanli ta gabatar da shawarar gina wani gidan ibada domin maye gurbin wannan wurin ajiye littattafan addinin Buddha. Don haka ta yi amfani da kudin da ta ajiye a boye wajen gina gidan ibada na Wanshousi, an kaurar da littattafan addinin Buddha zuwa gidan ibada na Wanshousi.'

Wannan kwararre ya kara da cewa, daga baya kuma, bayan da sarakunan kasar Sin na dauloli daban daban suka sha yi masa kwaskwarima, a karshe dai gidan ibada na Wanshousi ya zama babban gidan ibada na masarauta, inda aka iya kallon kyan ganin gidan ibada da fadar sarakuna da kuma lambu a wuri daya. Madam Sun Qiuxia, wata tafinta a gidan ibada na Wanshousi ta bayyana cewa,'A zamanin daular Ming da Qing, a matsayinsa na muhimmin gidan ibada na masarauta, sai muhimman jami'ai da kuma mambobin masarauta ne kawai suka iya shiga gidan ibada na Wanshousi. Sai ranar murnar haihuwar Buddha da kuma kwanaki da dama da ke bayan ranar, fararen hula sun iya samun izinin shiga wannan gida ibada domin nuna wa Buddha girmamawa.'

Babban zauren Daxiongbaodian da ke gaban gidan ibada na Wanshousi shi ne gini mafi muhimmanci a gidan ibada na Wanshousi. In an ci gaba da zuwa baya, sai an sadu da manyan duwatsu guda 3 da aka samu saboda gina wannan gidan ibada. An kuma gina babban zaure a kansu. Akwai kwaruruwa a tsakaninsu, an kuma hada su da gadojin dutse. A kewayensu an dasa bishiyoyi da yawa. Madam Chen Huilin, wadda ta zo daga lardin Taiwan na kasar Sin, a karo na farko ne ta kawo wa gidan ibada na Wanshousi ziyara, ta gaya mana cewa,'Ban yi tsammani cewa, akwai dakuna da yawan haka ba. An yi tsit a wajen, ko da yake akwai dogayen gine-gine a waje da shi. Na ji an ce, ana kiransa karamar fadar sarakuna ta kasar Sin. Kayayyakin da ake ajiyewa a wannan gidan ibada na da dogon tarihi.'

1 2