Nahiyar Afirka na da dimbin albarkatu da hamshakiyar kasuwa, saboda haka ne, akwai zarafin zuba jari da yawa a wannan shiyya. A fannin giggina muhimman ababen more rayuwa, kasashen Afirka da dama suna sanya ayyukan kyautata hanyar mota, da hanyar dogo, da filayen jiragen sama, da tashoshin jiragen ruwa, da samar da ruwa da wutar lantarki a gaban kome yayin da suke yunkurin farfado da tattlin arzikinsu. Kamar yadda wani manaja mai kula da harkokin kasashen Afirka na kamfanin hada-hadar kudi na bankin duniya ya ce, za a kashe kudin da yawansa ya kai dalar Amurka biliyan 250 wajen raya muhimman ababen more rayuwa a cikin nan da shekaru 10 masu zuwa a duk nahiyar Afirka.
Kazalika kuma, kasashen Afirka suna da kyakkyawar makoma a fannin raya ma'adinin man fetur. A halin yanzu dai, yawan gurbataccen man fetur da kasashen Afirka suke samarwa a kowace rana ya kai ganga kimanin miliyan 10, wanda ya tasam ma kashi 12 daga cikin dari na dukkan man fetur da ake samarwa a kowace rana a duniya.
A cikin 'yan shekarun nan, kasashen Afirka da dama suna daidaita manufofinsu kan albarkatun ma'adinai sannu a hankali ta fuskar yin gyare-gyaren dokar sana'ar hakar ma'adinai. Haka kuma, suna daukar jerin manufofin nuna gatanci a fannonin yin hayar kasa, da bada izinin hakar ma'adinai, da sayar da hada-hadar kayayyakin ma'adinai da dai sauran makamantansu, ta yadda za a bada kwarin gwiwa ga 'yan kasuwa baki da su zuba jari a kasashen Afirka Ban da wannan kuma, a wasu sabbin fannoni, kamar su sana'ar noma, da sana'ar yawon shakatawa, da kasuwar hada-hadar hannayen jari, kasashen Afirka suna shan kallo sosai daga 'yan kasuwa baki na kasashe daban-daban.(Murtala) 1 2
|