Assalam alaikum! Jama'a masu sauraro, barkanku da war haka! Barkanmu da kuma sake saduwa da ku a cikin shirinmu na yau na "Afirka a Yau". Za mu gabatar muku da wani bayanin musamman mai lakabi haka, halin zuba jari na nahiyar Afirka ya sami kyautatuwa sosai da sosai, kuma yana da kyakkyawar makoma mai haske.
Aminai masu sauraronmu, tare da bunkasar tattalin arziki da cigaban zaman karko na harkokin siyasa na kasashen Afirka daban-daban, makekiyar shiyyar Afirka ta rigaya ta zama wata shiyya ce dake jawo jarin waje mai yawan gaske, haka kuma, tana da kyakkyawar makoma wajen zuba jari a fannoni da dama, ciki har da giggina muhimman ababen more rayuwa, da raya ma'adinin man fetur, da bunkasa sana'ar noma, da daukaka cigaban kasuwannin yawon bude ido da hada-hadar hannayen jari.
Wani sharadi da aka gindaya wajen kyautata muhallin zuba jari na Afirka shi ne, a yi kokarin tabbatar da zaman karko a harkokin siyasa. Sakamakon kokarin da Majalisar Dinkun Duniya da gamayyar kasa da kasa suke yi tare cikin hadin gwiwa, wasu kasashen Afirka wadanda suke fama da tashe-tashen hankula da ya ki ci ya ki cinyewa, bi da bi ne suka sa aya ga rikice-rikcen, ciki har da Ruwanda, da Liberiya, da Angola, da Burundi, da Kwadivwa, da Uganda. Yanayin tsaro na wadannan kasashe ya kyautatu kwari da gaske, kuma kasashen sun fara wani yunkuri na neman wata hanyar da za su bi wajen bunkasa zamantakewar al'umma da tattalin arzikin. A halin yanzu dai, ko da yake akwai wasu abubuwan tada kayar-baya a wasu yankunan kasashen Afirka, amma dukkanin kasashen Afirka suna hankoron kawar da tarzoma, da shimfida zaman lafiya a duk shiyyar.
A waje daya kuma, tattalin arzikin Afirka yana cigaba cikin gaugawa yadda ya kamata. Dangane da wani rahoto mai suna "Hangen-Nesa kan Tattalin Arzikin Duniya" da asusun bada lamuni na IMF na kasa da kasa ya bayar a watan Oktoba na shekarar da ta shige, an ce, bunkasar tattalin arzikin kasashen Afirka dake kudancin hamadar Sahara a halin yanzu, ta fi sauri a cikin shekaru 40 ko fiye da suka gabata, wasu kasashen dake yankin sun cimma tudun-dafawa a fannin rage zaman talauci.
Kwamitin kula da harkokin cinikayya da bunkasuwa na MDD ya bayar da wani rahoto ranar 16 ga watan Oktoba na shekarar bara, inda ya bayyana cewar, yawan jarin waje da kasashen Afirka suka jawo kai tsaye a shekarar 2006, ya kai dalar Amurka biliyan 36, wato ya ninka sau daya idan an kwatanta shi da na shekarar 2004. Amma jama'a masu sauraronmu, ko kuna dai sane da cewar, yawan jarin waje da kasashen Afirka suka jawo a shekarun 1990 na karnin da ya gabata, ya kai dalar Amurka biliyan 6.2 kawai. Hakan ya biyo bayan da aka kara bukatar albarkatun halittu a duk fadin duniya, da kyautatuwar yanayin zuba jari na kasashen Afirka da dama. Bugu da kari, rahoton ya yi hasashen cewar, yawan jarin waje da kasashen Afirka suka jawo kai tsaye zai kara yin sama a shekarar da muke ciki.
1 2
|