Sin ciki da waje (chinaabc)Rediyon kasar SinSashen Hausa
China Radio International
Labarun gida
Labarun duniya
Labarun Siyasa
Labarun Tattalin Arziki
Labarun Al'adu
Labarun Wasanni
Sauran Labaru
Saurari labarai da dumi-duminsu da sauran shirye-shirye
more>>
[ Al'adu ]
 --Al'adun Sinawa
 --Kabilun kasar Sin
[ Bunkasuwa ]
 --Tattalin arziki
 --Bunkasuwar Sin
[ Yawon shakatawa ]
 --Yawo a kasar Sin
 --Wurare masu yawo
[ Ilmi, Lafiya ]
 --Fagen bincike
 --Kiwon lafiya
[ Wasanni ]
 --Labaran wasannin
 --Me ka sani
(GMT+08:00) 2008-01-09 18:53:43    
Manyan tsaunukan kankara mai laushi na Meili a lardin Yunnan

cri

Gari ya kara wayewa. Gajimaren da suka rufe manyan tsaunukan kankara mai laushi na Meili sun fara tafiya sannu a hankali. Wasu lokuta manyan tsaunukan da aka rufe su da fararen kankara mai laushi sun bullo a cikin gajimaren, wasu lokuta kuwa, sun buya. Kololuwar da ta bullo a farko, wato kololuwar Kawagebo, babbar kololuwar manyan tsaunukan kankara mai laushi na Meili, ta sake bacewa a cikin gajimaren.

Muna ta jira a wurin kallon, a karshe dai mun cimma burinmu. Hasken rana ya ratsa gajimare, dimbin gajimare ya wuce. Manyan tsaunukan kankara mai laushi na Meili sun fito a sararin sama sannu sannu. Hasken rana ya shafe manyan tsaunukan fararen kankara mai laushi da zinariya mai kyan gani. Madam Hu Dongmei ta zo nan daga lardin Sichuan yau da shekaru 6 da suka wuce. Kyan karkara na wurin ya burge ta sosai, yanzu ta kaddamar da wani shago domin karbar masu yawon shakatawa da kuma ci gaba da jin dadin kallon wannan kyan karkara, ta ce:

'A ganina wannan wuri na da kyau sosai, har ma ba na so na koma Sichuan. Mazaunan wurin na da budaddiyar zuciya, da sauki ne nake zama tare da su. Akwai ni'imtattun wurare a wajen, haka kuma, ana tabbatar da tsaron kai a wajen. Ko da dare, ba a bukatar a tsare mota.'

Kafin mu tashi komawa gida, mun sadu da wasu masu yawon shakatawa, mazaunan Beijing da suka dawo daga manyan tsaunukan, malama Xu Meng, ta gaya mana cewa:

'Mun kwana a wajen domin jiran kallon manyan tsaunukan kankara mai laushi na Meili, amma mun ci tura, shi ya sa muka shiga manyan tsaunuka. A kusa da kauyen Yubengcun, mun ga manyan tsaunukan kankara mai laushi guda 2. Amma da kyar muka ga kololuwar Kawagebo. Ita ce kololuwa mai tsarki a idon 'yan kabilar Zang. A ganin 'yan kabilar Zang, wadanda suka ganta mutane ne da suka taki sa'a. In kun sami dama, za ku iya zuwa wannan kololuwa mai tsarki, tana da kyan gani sosai.'

Bayan ziyara mai tsawon kwanaki da dama, mun fahimci wani karamin bangaren kyan ganin manyan tsaunukan kankara mai laushi kawai, da za mu tuna da shi a zukatansu kawai. (Tasallah)


1 2