Sin ciki da waje (chinaabc)Rediyon kasar SinSashen Hausa
China Radio International
Labarun gida
Labarun duniya
Labarun Siyasa
Labarun Tattalin Arziki
Labarun Al'adu
Labarun Wasanni
Sauran Labaru
Saurari labarai da dumi-duminsu da sauran shirye-shirye
more>>
[ Al'adu ]
 --Al'adun Sinawa
 --Kabilun kasar Sin
[ Bunkasuwa ]
 --Tattalin arziki
 --Bunkasuwar Sin
[ Yawon shakatawa ]
 --Yawo a kasar Sin
 --Wurare masu yawo
[ Ilmi, Lafiya ]
 --Fagen bincike
 --Kiwon lafiya
[ Wasanni ]
 --Labaran wasannin
 --Me ka sani
(GMT+08:00) 2008-01-09 18:53:43    
Manyan tsaunukan kankara mai laushi na Meili a lardin Yunnan

cri

Masu sauraro, barkanku da war haka. Ni ce Tasallah da ke jan akalar wannan shiri na yawon shakatawa a kasar Sin. Yau ma bari mu ziyarci wasu manyan tsaunukan kankara mai laushi da ke kan iyakar lardin Yunan da jihar Tibet mai cin gashin kanta a kudu maso yammacin kasar Sin. Daga bisani kuma, za mu ci gaba da ziyarar filayen wasa na gasar wasannin Olympic ta Beijing.

Manyan tsaunukan kankara mai laushi na Meili da ke yankin Diqing na kabilar Zang mai cin gashin kansa manyan tsaunuka ne masu tsarki a idanun 'yan kabilar Zang mazaunan wurin, haka kuma wuri ne da mabiya addinin Buddha irin na Tibet suka yi aikin hajji. Akwai manyan duwatsu guda 13 a wajen, wadanda matsakaicin tsayinsu ya wuce mita dubu 6 daga leburin teku. Tsayin babbar kololuwarsu wato Kawagebo ya wuce mita dubu 6 da dari 7, ya zuwa yanzu babu wanda ya isa kololuwarsa ba tukuna.

Bayan tashi daga gundumar Shangri-la, babban birnin yankin Diqing, motarmu ta kama hanyar mota ta Dianzang, tana tafiya a tsakanin manyan tsaunuka da kuma gajimaren da ke kewayen manyan tsaunukan. A lokacin da motar ta shiga gajimare a wani lokaci, ba mu iya kallon ni'imtattun manyan tsaunuka sosai ba. A kan hanyarmu ta zuwa manyan tsaunukan kankara mai laushi, ko wane mutum ya iya more idonsa da kyan karkara. A lokacin hutu, wakilinmu ya yi hira da malam Yuan Liuwen, wani direba na wurin, wanda ya yi shekaru fiye da 20 yana tukin mota, ya ce:

'Yawancin masu yawon shakatawa da suka kawo garinmu ziyara sun fi nuna sha'awarsu kan ziyarar manyan tsaunukan kankara mai laushi. Idan ka kawo wa jihar Tibet ziyara, ka iya shiga jihar Tibet ta hanyar nan, wato hanyar mota ta Dianzang, amma bayan tsakiyar kwanaki 10 na watan Nuwamba, ka gaza shiga jihar Tibet domin fuskar hanyar ta fara daskarewa.'

'Yan kabilar Zang suna nuna girmamawa ga manyan tsaunukan kankara mai laushi na Meili. A ko wace shekara, dimbin fararen hula 'yan kabilar Zang su kan kawo wa manyan tsaunukan kankara mai laushi na Meili ziyara, su kan kewaye shi domin nuna girmamawa.

Kashegari misalin karfe 6 da sassafe, mun isa wurin kallo na gidan ibada na Feilaisi. Ko da yake gari bai waye ba tukuna, amma wasu masu yawon shakatawa da suka nemi kallon manyan tsaunukan kankara mai laushi da kuma mazaunan yankunan karkara da ke zama a kusa da gidan ibadan sun taru a wajen. A sararin sama a nesa, kololuwar wani farin babban dutse ta bullo a cikin gajimare, sai ka ce tana kasancewa a sararin sama. Mutane su kan nuna girmamawa a zukatansu saboda ganin irin wannan kyan karkara. Madam Zhong Ning, wata budurwa da ta zo daga birnin Guangzhou da ke kudancin kasar Sin, ita da abokanta suna jiran bullowar manyan tsaunukan kankara mai laushi na Meili. Ta gaya mana cewa:

'Na zo nan tare da abokaina domin kallon manyan tsaunukan kankara mai laushi da kuma yin yawon shakatawa. Mun yada zango a wajen a jiya da dare. Ba safai yanayi ya kan yi kyau hakan ba. Na ji farin ciki sosai saboda yau ba a yi ruwan sama ba.'


1 2