Ban da wannan kuma, mutanen da ba su taba shan taba ba, amma suna zama tsakanin masu shan taba kullum su ma sun fito da alamar kamuwa da ciwon sukari, yawansu ya kai misalin kashi 17 cikin dari, wadanda suka taba shan taba, amma daga baya ba su ci gaba da shan taba ba da yawansu ya kai misalin kashi 14 cikin dari sun fito da alamar kamuwa da ciwon sukari. Mutanen da ba su taba shan taba ba, kuma ba su zama tsakanin masu shan taba ba da yawasu ya kai misalin kashi 11.5 cikin dari sun fito da irin wannan alama.
Rahoton ya ce, mai yiwuwa ne dafin da aka samu a lokacin da taba ya kone zai tattara a cikin wani kayan ciki na mutum, wanda ya samar da insulin, amma ana bukatar cin gaba da yin nazari kan wannan bayani.
Sa'an nan kuma, rahoton bincike ya nuna cewa, mai yiwuwa ne barazananr da zama tsakanin masu shan taba yake kawo wa mutane ta fi wadda aka kiyasta. Hayakin da aka samar da shi a lokacin shan taba ya sanyayu a cikin iska, ya kuma canja kansa, a sakamakon haka, hayakin da mutane suka numfashi ya kunshe da dafi ya fi yawa, in an kwatanta shi da wanda masu shan taba suka numfashi kai tsaye. (Musa Guo) 1 2
|