Bisa sakamakon binciken da kasar Poland ta yi, shan taba zai kawo illa ga zuciyar matasa, kafin wannan kuma, an taba ganin cewa, shan taba ba zai yi mummunan tasiri ga zukatan matasa ba.
Bisa wani rahoton da wata mujalla ta kasar Amurka ta yi, 'yan kimmiya na jami'ar likita ta Warsaw na kasar Poland sun yi nazari kan mutane 66 masu shan taba wadanda ke da shekaru 20 zuwa 40 da haihuwa, dukkansu sun riga sun sha taba har shekaru 6 zuwa 20, kuma yanzu suna shan tabai 15 zuwa 25 a ko wace rana.
Masu bincike sun sa ido kan zukatansu ke ciki bayan awoyi biyu da sha taba, sun gano cewa, dukkkan zukatansu suna da matsala, ba su aiki kamar yadda ya kamata ba.
Masu binciken sun ce, wannan bincike ya nuna cewa, shan taba zai kawo illa ga zukatan matasa kamar ya yi wa sauran mutane, idan zukatan matasa ba su aiki yadda ya kamata ba, watakila za su kamu da ciwon zuciya mai tsanani nan gaba.
Yanzu za mu soma gabatar muku da labarin da muka shirya muku. Bisa rahoton bincike da 'mujallar ilmin aikin likita ta kasar Birtaniya' ta bayar a kwanan baya, an ce, ba ciwon zuciya da ciwon kansa kawai ba, mai yiwuwa ne shan taba zai iya haifar da ciwon sukari. Duk da mutanen da suke shan taba da kansu, ko kuma wadanda ba su sha taba ba, amma suna zama tsakanin masu shan taba kullun, an tilasta musu shan taba.
Wata cibiyar nazarin ilmin aikin likita ta Birmingham ta kasar Amurka ta yi bincike kan halin da mutane kimanin 4500 suke ciki a fannin lafiyarsu a biranen Birmingham da Chicago da dai sauransu a shekarar 1985 da ta 2000. Sakamakon da aka samu ya nuna cewa, tun daga shekarar 1985 zuwa ta 2000, masu shan taba da yawansu ya kai kashi 22 cikin dari sun fito da alamar kamuwa da ciwon sukari. Dalilin da ya sa kamuwa da ciwon sukari shi ne jikin mutum bai iya samar da wani abu mai suna insulin a bakin Turawa ba, wanda ya iya kyautata sukari a cikin jinin mutum.
1 2
|