Sin ciki da waje (chinaabc)Rediyon kasar SinSashen Hausa
China Radio International
Labarun gida
Labarun duniya
Labarun Siyasa
Labarun Tattalin Arziki
Labarun Al'adu
Labarun Wasanni
Sauran Labaru
Saurari labarai da dumi-duminsu da sauran shirye-shirye
more>>
[ Al'adu ]
 --Al'adun Sinawa
 --Kabilun kasar Sin
[ Bunkasuwa ]
 --Tattalin arziki
 --Bunkasuwar Sin
[ Yawon shakatawa ]
 --Yawo a kasar Sin
 --Wurare masu yawo
[ Ilmi, Lafiya ]
 --Fagen bincike
 --Kiwon lafiya
[ Wasanni ]
 --Labaran wasannin
 --Me ka sani
(GMT+08:00) 2008-01-09 12:23:04    
Kungiyar wasan guje-guje da tsalle-tsalle ta kasar Sin tana share fagen gasar wasannin Olympic ta Beijing cikin himma

cri

Ko da yake kasar Sin ta sami wasu nasarori da kuma ci gaba a wasan guje-guje da tsalle-tsalle a shekarar bara, haka kuma, tana gudanar da aikin horaswa na lokacin dari yadda ya kamata a yanzu, amma a baya ne take bisa sauran kasashen duniya da suka nuna fifiko a wasan guje-guje da tsalle-tsalle, wato yana kasancewa da babban gibi a tsakaninsu. Game da matsayin kasar Sin a duniya a wasan guje-guje da tsalle-tsalle, har kullum Mr. Feng yana kasancewa cikin natsuwa, shi ya sa ya sifanta kalubalen da kungiyar wasan guje-guje da tsalle-tsalle ta kasar Sin ke fuskanta a gun gasar wasannin Olympic ta Beijing a wannan shekara da hakan 'tana daukar babban nauyi, kuma tana fuskantar hali mai tsanani'. Ya ce,'A galibi dai, yanzu an rage watannin da ba su kai 8 da bude gasar wasannin Olympic ta Beijing ba. A cikin irin wannan gajeren lokaci, an danka mana babban nauyi game da samun maki mai kyau a gun gasar wasannin Olympic ta Beijing, muna fuskantar hali mai tsanani. Muhimman dalilan da suka sa hakan su ne, da farko ba mu da isasshen karfi. Shirye-shiryen da muke kan gaba a duniya da kuma 'yan wasanmu da suke matsayin mafiya nagarta 10 a duniya ba su yi yawa ba. Na biyu kuma, ya kamata mu lura da cewa, a cikin ko wane shiri, a ciki har da wanda 'yan wasanmu suke nuna fifiko, muna fuskantar abokan karawa masu karfi. Kada mu kyale wannan batu.'(Tasallah)


1 2