Don share fagen gasar wasannin Olympic ta Beijing a shekarar da muke ciki, yanzu kungiyar wasan guje-guje da tsalle-tsalle ta kasar Sin tana samun aikin horaswa na lokacin dari daga dukkan fannoni, kuma ta shiga muhimmin wa'adi wajen kyautata karfin 'yan wasa da jikinsu da kuma inganta fasaharsu.
Lalle kasar Sin ta sami nasarori da yawa a wasan guje-guje da tsalle-tsalle a shekarar 2007. Game da dalilin da ya sa kasar Sin ta sami wadannan nasarori, Feng Shuyong, babban malamin horas da wasanni na kungiyar wasan guje-guje da tsalle-tsalle ta kasar Sin ya yi mana nazari cewa,'A ganina, nasarorin da muka samu suna da nasaba da kokarin da muke ta bayarwa a shekarun baya sosai. A shekarun nan da suka wuce, mun dora muhimmanci kan nazarin ka'idojin wasanni da sigogin musamman, ta haka, malaman horas da wasanni sun kara saninsu kan ka'idoji da sigar musamman ta ko wane shiri, sun horar da 'yan wasa daidai bisa halin da 'yan wasa ke ciki.'
Nasarorin da ta samu a shekarar 2007 sun bai wa kungiyar wasan guje-guje da tsalle-tsalle ta kasar Sin babban karfin gwiwa, sun kuma aza harsashi a gare ta wajen kara samun maki mai kyau. Yanzu 'yan wasa na kungiyar wasan guje-guje da tsalle-tsalle ta kasar Sin suna nan suna samun aikin horaswa na mataki na farko a wurare daban daban na kasar Sin. Wannan ne karo na karshe da suka sami aikin horaswa a lokacin dari kafin gasar wasannin Olympic ta shekarar 2008. Aikin horaswa da suke samu a yanzu yana da nasaba da makin da za su samu a gun gasar wasannin Olympic, shi ya sa Mr. Feng ya mayar da wannan aikin horaswa a matsayin mataki na gaggauta share fagen gasar wasannin Olympic, ya ce,'Yanzu watanni kusan 2 sun wuce, a galibi dai an sami sakamako mai kyau daga wajen aikin horaswa na lokacin dari, ya zuwa yanzu dai mun nuna gamsuwa. Yawancin 'yan wasanmu sun kammala ayyukansu a cikin mataki na farko. Sa'an nan kuma, mun cimma tudun dafawa a fannin warkar da wadanda suka jikkata, ko kuma suke fama da ciwo.'
In an tabo magana kan wasan guje-guje da tsalle-tsalle na kasar Sin, to, mutane su kan tuna da dan wasa Liu Xiang na kasar Sin, wanda shi ne zakara a cikin gasar gudu tare da ketare shinge mai tsawon mita 110 a gun gasar wasannin Olympic ta Athens.
Gasar wasannin Olympic ta Beijing tana zuwa, tana bakin kofar gidanmu. Yanzu a karkashin jagorancin Mr. Sun Haiping, malaminsa na horas da wasanni, Liu Xiang ya kaddamar da aikin horaswa na lokacin dari a nan Beijing tun daga makon jiya daga birnin Shanghai. Aikin horaswa na wannan mataki na da matukar muhimmanci wajen kyautata jikin Liu Xiang da kuma samun maki mai kyau a shekarar bana, shi ya sa Liu Xiang da malaminsa suka fi dora muhimmanci kansa. Mr. Sun ya ce,'A galibi dai, ina gamsuwa da aikin horaswa da Liu Xiang yake yi. Ya fi yin aiki tukuru a wasu fannoni bisa na shekarun baya. Saboda a matakin da ya gabata, a Shanghai, Liu Xiang bai sanya takalman gasa ba a lokacin horo. Bayan da ya iso Beijing, a karo na farko ya sanya takalman gasa a lokacin horo. Sanya takalman gasa ya ba da taimako wajen kara yin aikin tukuru a gare shi.'
1 2
|